Bayani: Me yasa kayayyaki ke ƙara tsada a kasuwanni duk da hauhawar farashi ya sauka

Bayani: Me yasa kayayyaki ke ƙara tsada a kasuwanni duk da hauhawar farashi ya sauka

  • A ranar Litinin na wannan makon ne hukumar kididdiga na kasa NBS ta fitar da alkalluman tattalin arzikin Najeriya
  • Alkalluman sun nuna hauhawar farashin ya sauka da amma farashin kayayyaki a kasuwanni suna sauka ba wasu ma kara tsada suke yi
  • Masanin tattalin arziki ya yi fashin baki kan dalilin da yasa kaya a kasuwa ba su sauka ba duk da duk da alkalluman sun nuna akasin haka

A ranar Litinin ne Hukumar Kididdiga ta Kasa, NBS, ta fitar da rahoton ta na hauhawar farashin kaya na watan Oktoban 2021, tun bayan fitowa rahoton, 'yan Nigeria na tambayoyin game da ainihin abin da rahoton ke nufi.

Mutane na tambayoyi da cecekuce kan rahoton ne domin farashin kaya ba su sauka ba a kasuwanni amma rahoton ya ce hauhawar farashin ya yi kasa.

Kara karanta wannan

N2.3tr muka ware don rabawa yan Najeriya kayan tallafin Korona, Gwamnatin tarayya

A cewar rahoton, alkalluman CPI da ke auna sauyin da ake samu a farashin kayayyaki da ayyuka ya na cigaba da sauka karo na bakwai a jere da 15.99 cikin 100 a Oktoba.

Bayani: Me yasa kaya ke ƙara tsada a kasuwanni duk da hauhawar farashi ya sauka
Abin da yasa kayayaki ba su yi sauki ba a kasuwa duk da hauhawan farashin ya yi kasa. Hoto: Forbes

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Menene dalilin da yasa farashin kaya a kasuwanni bai sauka ba

Wakilin Legit.ng Hausa ya tattauna da wani masanin tattalin arziki daga kamfanin One 17 Investment Capital, mai suna Ismail Rufai inda ya yi fashin baki kan yadda lamarin ya ke.

Ya ce da gaske ne farashin kaya ba su sauka ba duk da cewa alkalluman hauhawan farashin ya sauka, sai dai ya kamata a gane yadda NBS ke yin wannan lissafin.

"NBS na kwatanta hauhawar farashin ne na yanzu da shekarar da ta gabata misali watan Agustan 2021 da na Agustan 2020.
"Idan hauhawar aka samu a bana a tsakanin lokacin bai kai na bara ba, sai a ce an samu faduwar hauhawar farashi ko da a kasuwa farashi bai ragu ba," in ji shi.

Kara karanta wannan

Nan da watanni uku ku kara kudin man fetur: Bankin duniya ga Gwamnatin Najeriya

Ya cigaba da cewa akwai alkalluma biyu da NBS ke amfani da su wurin lissafin da suka hada da Food Index - mai lissafa farashin kayan abinci da Core Index - da ke lissafa farashin sauran kayayyaki amma banda kayan abinci da makamashi.

Rahoton ya nuna cewa an samu hauhawar farashin kayayyaki kamar gas din girki, tufafi, zirga-zirgan jirgin sama, motocci, kayan lantarki na gida, kudin asibiti da sauransu inda ya ce mafi yawancinsu daga kasashen waje ake shigo da su.

Amma a bangaren kayan abinci, hauhawar farashin a kasuwa ya faru ne galibi saboda rashin tsaro, canjin kudi da sauransu.

Ya ce:

"Alkalluman suna kwatanta hauhawar farashin da na shekarar da ta gabata misali hauhawar farashin Oktoban 2020 da na 2021."

Ta yaya NBS ke samun alkalluman

Rufai ya ce NBS tana da masu tattara mata rahoto kimanin su 10,534 a sassa daban na kasar da ke binciko farashin kayayyaki da ayyuka.

Kara karanta wannan

Ba mu da hurumin daidaita farashin gas din girki, Gwamnatin tarayya

NBS na amfani ne da farashin wasu kayayyaki da ayyuka 740 da mutane suka fiye amfani da su wurin lissafin ta, don haka lissafinta dai-dai ne bisa alkalluman da ta yi amfani da su.

Menene mafita?

Masanin ya ce muddin kasa ta dogara da siyan kayayyaki daga kasashen waje fiye da abin da ta ke sayarwa tabbas darajar kudinta zai rika raguwa.

Hakazalika, wasu yan kasuwan suna boye kayan abinci har sai ya yi tsada kafin su fitar da shi kasuwa su sayar, sannan akwai matsalar tsaro da rashin tallafawa manoma da gwamnati ba ta yi.

Ya shawarci gwamnati ta tabbatar an samu tsaro a kasa ta yadda manoma za su koma gona sannan ta rika tallafa musu da bashi, iri na zamani, dabarun noman zamani, taki da sauransu.

Dangote da MTN ne kamfanonin da suka fi biyan haraji a Nigeria, jimillar kudin da aka samu N289.4bn

A wani labain, kun ji cewa kamfanin Simintin Dangote ya zama kamfanin da ya fi ko wanne kamfani biyan kudi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Yadda ‘yan mata 7 da ke dawowa daga Maulidi suka rasu a hatsarin jirgin ruwa a Jigawa

Fittacen kamfanin mai kera siminti a Nigeria ya zama na farko cikin jerin kamfanoni 152 da hukumar kasuwanci ta Nigeria, NGX, ta lissafa a watanni shida na farkon 2021.

A cikin watanni 6 na farkon 2021, Kamfanin Simintin Dangote da wasu kamfanoni 13 da ke kasuwanci a NGX sun biya harajin N289.4b ga hukumar FIRS da wasu hukumomin da su samarwa gwamnati kudin shiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel