Dangote da MTN ne kamfanonin da suka fi biyan haraji a Nigeria, jimillar kudin da aka samu N289.4bn

Dangote da MTN ne kamfanonin da suka fi biyan haraji a Nigeria, jimillar kudin da aka samu N289.4bn

  • Kamfanoni guda 13 da suke hada-hada a hukumar hada-hada ta Nigeria, NGX, sun biya jimillar haraji na Naira Biliyan 289.4
  • Hukumar tattara kudaden shiga na tarayya, FIRS, tana daya daga cikin hukumomi da ke karbar haraji kuma a kwanan nan ta bayyana cewa ta samu kudaden da ya wuce hasashen da ta yi cikin wata 8 na farkon 2021
  • A bisa doka, ya kamata kamfanonin da ke ayyukansu a Nigeria su rika biyan harajin kudi, harajin Ilimi, harajin NITDA da harajin asusun hukumar yan sanda

Kamfanin Simintin Dangote ya zama kamfanin da ya fi ko wanne kamfani biyan kudi a Najeriya.

Fittacen kamfanin mai kera siminti a Nigeria ya zama na farko cikin jerin kamfanoni 152 da hukumar kasuwanci ta Nigeria, NGX, ta lissafa a watanni shida na farkon 2021.

Kara karanta wannan

Hukumar NYSC ta koka kan kudin abinci: N650 ga 'yan NYSC, N1000 ga fursunoni

A cikin watanni 6 na farkon 2021, Kamfanin Simintin Dangote da wasu kamfanoni 13 da ke kasuwanci a NGX sun biya harajin N289.4b ga hukumar FIRS da wasu hukumomin da su samarwa gwamnati kudin shiga.

Kamfanin Simintin Dangote ya biya gwamnatin tarayya zunzurutun kudi Naira biliyan 89.62, an samu karin 144% kan abinda kamfanin ya biya na N36.71bn a shekarar 2020.

Dangote da MTN ne kamfanonin da suka fi biyan haraji a Nigeria, jimmilar kudin da aka samu N289.4bn
Dangote da MTN ne kamfanonin da suka fi biyan kudin haraji a Nigeria, jimmilar kudin da aka samu N289.4bn. Hoto: Tom Saater
Asali: Getty Images

Sauran kididdigar

Kamfanin MTN Nigeria wanda ya zama kamfani na 2 a biyan haraji, ya samar da Naira Biliyan 73.29 a H1 2021, wanda ya zama karin kaso 64% daga Naira biliyan 44.69 da aka ruwaito a H1 2020.

Yayin da bankin United Bank for Africa ya biya harajin Naira Biliyan 15.06 daga Naira Biliyan 12.7 da ya biya a H1 2020.

Kara karanta wannan

Hameed Ali zai tarawa Gwamnatin Buhari harajin Naira Tiriliyan 2 a cikin shekara daya

Guaranty Trust Holding Co PLC, duk da cewa shi ya zo na uku ya biya Naira Biliyan 13.64 a H1 2021, hakan na nufin an samu ragin 12% daga Naira Biliyan 15.44 da ya biya a H1 2020.

An samu bayanai a kan yadda Access Bank ya biya harajin Naira Biliyan 10.56 a H1 2020 daga Naira Biliyan 13.27 a H1 2020.

Zenith Bank Plc ya biya harajin Naira Biliyan 10.94 a H1 2020, karin 6.2% daga Naira Biliyan 10.3 a H1 2020.

A dayan bangaren kuwa, akwai FBN Holdings da ya biya harajin Naira biliyan 7.15 a H1 2020 karin 24% akan Naira biliyan 5.77 a H1 2020.

Nestle Nigeria Plc sun biya harajin Naira Biliyan 11.65 a H1 2020 a bangaren kayan amfanin jama’a masu saurin shiga (FCMG), ragin 3.2% daga Naira biliyan 12.04 da aka ruwaito a H1 2021.

An amshi harajin Nigerian Breweries Plc da Guinness Nigeria Plc a H1 2021 na Naira Biliyan 4.2 da 4.5 ko wanne.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya yi basaja ya kai ziyaran bazata asibiti, ya damke ma'aikata na karban kudin Haram

Sai kuma Lafarge Africa Plc da harajin su ya karu da 55% daga N8.43b a H1 2021 daga N5.4b na H1 2020, yayin da Kamfanin Simintin BUA ya biya harajin N6.3b a H1 2021, karin 45% daga N4.35b da aka ruwaito a H1 2020.

Abuja: Yadda tsadar 'Pure water' ya sa mazauna birnin tarayya suka koma shan ruwan famfo

A wani labarin, kun ji cewa wasu mazauna babban birnin tarayya, Abuja sun koma shan ruwan famfo maimakon fiya wata saboda tsadar rayuwa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A binciken da NAN ta gudanar ta gano cewa yanzu haka kudin fiya wata ya nunka kansa, don maimakon N10 ko wacce leda, yanzu ta koma N20.

Mazauna yankin da su ka tattauna da NAN sun bayyana yadda a baya suke siyan fiya wata saboda yadda su ka yarda da ingancin sa fiye da na famfo.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi tafiya, Osinbajo ya jagoranci FEC, an amince a kashe N47bn a kan wasu ayyuka

Asali: Legit.ng

Online view pixel