Ba mu da hurumin daidaita farashin gas din girki, Gwamnatin tarayya

Ba mu da hurumin daidaita farashin gas din girki, Gwamnatin tarayya

  • Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ba ta da hurumin daidaita farashin iskar gas na girki a kasar nan saboda kasuwannin duniya ne ke hakan
  • Karamin ministan man fetur, Timipre Sylva, ya ce shugaban kasa Buhari ya fada tsananin damuwa ganin halin da jama'a ke ciki
  • Shugaban kasan ya sha alawashin yin wani abu a kan farashin gas din duk da har a Turai ya tashi ba Najeriya kadai ba

Aso Villa, Abuja - Gwamnatin tarayya a ranar Talata ta ce ba ta da hurumin daidaita farashin iskar gas ta girki saboda abu ne wanda kasashen duniya ke daidaitawa.

Karamin ministan man fetur, Timipre Sylva, wanda ya sanar da hakan ga manema labarai na gidan gwamnati, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fada damuwa sakamakon tashin farashin gas din girkin, Tribune Online ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kada ka janye dokar hana shigo da shinkafar kasar waje, Gwamnan APC ga Buhari

Ba mu da hurumin daidaita farashin gas din girki, Gwamnatin tarayya
Ba mu da hurumin daidaita farashin gas din girki, Gwamnatin tarayya. Hoto daga Tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Ministan man fetur din ya je fadar shugaban kasa da ke Abuja inda ya gabatar masa da Injiniya Faruk Ahmed, shugaban NMDPRA da Injiniya Gbenga Komolafe shugaban NUPRC.

Ya ce farashin iskar gas ya dogara ne da kasuwar duniya duk da ya ce gwamnati za ta yi duk abinda ya dace wurin zabtare farashinsa ballantana a lokacin Kirsimeti.

Kamar yadda TheCable ta ruwaito, ya ce, "dole ne mu fahimci cewa ba a tallafin farashin iskar gas ta girki. A don haka ba farashin da gwamnati ta ke saisaitawa ba ne. A gaskiya duniya ce ke saisaita farashin.
"Kuma duk kun san cewa ko a Turai farashin iskar gas ta girki ya tashi. Har rikici aka dan samu a kan hakan a Turai. Don haka farashinsa na duniya ne baki daya ba wai kasar nan ba."

Kara karanta wannan

Sheikh Pantami ya yi martani kan fastocinsa dake yawo na takarar shugaban kasa a 2023

Sylva ya bayyana cewa shugaban kasan ya umarcesa da ya garzaya Nembe da ke jihar Bayelsa domin duba yanayin barnar da zubar gas a yankin ta janyo.

Ministan ya ce zai ziyarci yankin da lamarin ya shafa a ranar Laraba domin duba yanayin barnar.

Hawan farashi: Ana hasashen tsadar iskar gas zai kai N10k a 12.5 nan gaba kadan

A wani labari na daban, jaridar Punch ta ruwatio cewa, masana sun gargadi 'yan Najeriya cewa nan ba da jimawa ba za su fara siyan iskar gas a kan farashi mai tsananin tsada. Wannan kenan a cewar 'Yan kasuwa na Iskar Gas.

'Yan kasuwar sun nuna damuwar su kan karancin shigo da gas da ke haifar da hauhawar farashinsa.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa, 'yan kasuwan sun yi gargadin cewa iskar gas mai nauyin kilo 12.5 da a halin yanzu ake sayar dashi sakanin N7,500 zuwa N8,000 na iya tashi zuwa N10,000 kafin watan Disamba idan ba a yi wani abu don magance tsadar ba.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An tsinta gawar limamin Abuja kusa da gona

Asali: Legit.ng

Online view pixel