Yan Najeriya sun yi martani kan wani matashi da ya ci F9 a darussan NECO, Ya kammala digiri da darajar farko

Yan Najeriya sun yi martani kan wani matashi da ya ci F9 a darussan NECO, Ya kammala digiri da darajar farko

  • Wani matashi ya nuna farin cikinsa da kammala digiri bayan ya ci F9 a darussan NECO da ya zauna karon farko
  • Mayowa Joshua Amusan ba shi kaɗai ya kammala digiri da sakamako mai daraja ta farko a jami'ar Ibadan ba amma shine dalibi mafi hazaka a sashinsa
  • Mayowa ya rubuta jarabawar WAEC sau uku kafin ya samu sakamakon da yake bukata, yace yaji tsoron neman jami'a saboda gaza cin jarabawa

Wani ɗalibi da ya kammala digiri, Mayowa Joshua Amusan, ya bayyana tsantsar farin cikinsa a kafar sada zumunta bayan samun nasara a karatunsa.

Mayowa ya kammala karatu da sakamako mai daraja ta farko a jami'ar Ibadan, kuma shine ɗalibi mafi kwazo a sashin koyon tattalin noma (Agricultural Economics).

Kara karanta wannan

Yadda dan Najeriya ya zama sanata a Turai, ya kware a girki, kuma yake so ya gaji Buhari

Joshua Amusan
Yan Najeriya sun yi martani kan wani matashi da ya ci F9 a darussan NECO, Ya kammala digiri da darajar farko Hoto: Linkedln/Joshua Mayowa Amusan
Asali: UGC

Ya samu F9 a baki ɗaya darussan NECO

Da yake bayyana murnarsa a Linkedln, Mayowa yace ya samu F9 a baki ɗaya a darussan jarabawar fita daga sakandire ta farko da ya zauna, itace NECO.

Da yake nuna kwafin takardan sakamakon F9 da ya samu, Mayowa ya kara da cewa sai da ya zauna WAEC sau uku kafin ya ci dukkan darussa.

Matsahin ya shaida cewa ya cigaba da karatunsa a kwalejin fasaha dake Ibadan, babban birnin Oyo.

Na samu gurbi a UI kai tsaye

A kwalejin fasaha dake Ibadan, Mayowa ya nuna basirar da Allah ya masa, inda ya kammala da sakamako ma fi kyau kuma ya yanke shawaran zarcewa jami'ar Ibadan (UI).

Sabida matsalar gaza cin jarabawarsa, Mayowa yace yaji ɗar-ɗar wajen rijistan Post UTME na UI domin yana tsoron gaza kai bantensa.

Kara karanta wannan

Ra'ayi: Bidiyon matashin da ya bar sana'a ya koma zaman don kallon jiragen kasa

Ƙarfin guiwar iyalai na da yan uwa, yasa na zauna jarabawan kuma nasamu gurbi a kwas ɗin Agricultural Economics, inji shi.

Matashin yace:

"Iyaye na, yayye da kanne na suna da yaƙini a kaina, kuma da taimakon Allah na samu gurbi ta kai tsaye zuwa aji biyu a kwas din Agric. Economics."
"Bayan sakamako mai daraja ta farko da na samu, ni na zama ɗalibi mafi kwazo a kwas ɗin mu. Da taimakon Allah, aiki tukuru, masoyan iyalai, da abokai na gari komai ya zamo mai sauki."

Martanin yan Najeriya

Legit.ng Hausa ta tattaro muku yabon da wannan matashi ya sha daga bakunan yan Najeriya.

Topah grace Osuashi tace:

"Ina son dagiya, haka ya tuna mun wata maganar masu basira a makaranta, 'Kar ka amince da faɗuwa, idan ka yi rashin nasara, sake gwadawa."

Ar. Adedayo Jeremiah Adeyekun yace:

"Duk wanda kaga ya yi rashin nasara shi yaso. Rashin cikakken shiri da kuma kafiya kan abinda ka tasa, shike kawo rashin nasara."

Kara karanta wannan

Sheikh Pantami ya yi martani kan fastocinsa dake yawo na takarar shugaban kasa a 2023

"Ina taya ka murna, kuma ka tabbata wannan nasara taka ta ɗore har zuwa gaba."

Abdullahi Salawu yace:

"Wannan babban nasara ce Mayowa. Dan Allah ka amshi taya murna ta, nasan abinda ke tattare da shiga jami'a kai tsaye. Kasancewa mai hazaka ba shine kaɗai ba, sai da kafiya da sadaukarwa."

A wani labarin kuma Yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu kan wata hazikar yarinya da ta ci A a WAEC, ta samu 345 a Post UTME

Wata yar Najeriya daga jihar Imo, Chiemela Stephanie Madu, ta samu sakamako mai daraja ta farko a dukkan darussan da ta zauna a WAEC.

Yarinyar ta samu nasarar cin maki 345 cikin 400 a jarabawar share fagen shiga jami'a Post UTME a jami'ar FUTO.

Asali: Legit.ng

Online view pixel