Shirin kidayan yawan yan Najeriya zai lakume sama da Biliyan N190bn a 2022, Majalisa

Shirin kidayan yawan yan Najeriya zai lakume sama da Biliyan N190bn a 2022, Majalisa

  • Majalisar dattawan Najeriya ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ware sama da biliyan N190bn domin gudanar da kidaya a 2022
  • Shugaban kwamitin kidaya da katin bayanan ɗan kasa, Sanata Sahabi, yace majaalisa zata jira sanarwan shugaban kasa kan ranar fara wa
  • Yace duk da kasancewar 2022 ta yi kusa da babban zaɓen dake tafe, amma yasan cewa FG ta yi lissafi kafin ta zaɓi shekarar

Abuja - Kwamitin kidaya na majalisar dattijan tarayyan Najeriya, a ranar Laraba ya bayyana cewa an ware sama da biliyan N190bn domin gudanar da kidaya a shekara mai zuwa.

Dailytrust tace shugaban kwamitin, Sanata Sahabi Alhaji Yaú, shine ya bayyana haka ga manema labarai bayan kare kasafin kudin 2022 na hukumomin dake karkashin kulawar kwamitinsa.

Majalisar dattawa
Shirin kidaya yawan yan Najeriya zai lakume sama da Biliyan N190bn a 2022, Majalisa Hoto: Nigerian Senate FB Fage
Asali: Facebook

Sanata Sahabi yace:

"Gwamnati ta ware makudan kudi sama da biliyan N190bn domin gudanar da kidayar gano yawan yan Najeriya."

Kara karanta wannan

Zamu nunawa yan Najeriya cewa PDP ta canza, Gwamnan jihar Oyo

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A halin yanzun zamu jira, mu zuba ido mu ji sanda shugaban ƙasa Buhari zai bayyana lokacin fara shirin."

Meyasa sai a 2022?

Gwamnatin tarayya ta zabi gudanar da shirin kidaya a shekara mai zuwa wato 2022 duk da kasancewar ta yi kusa da babban zaɓen 2023.

Game da zaɓen 2022, shugaban kwamitin, Sanata Sahabi ya ƙara da cewa:

"Suna ganin wannan shekarar ita ce ta fi dacewa a gudanar da shirin, tabbas sun buga lissafin su ne yasa suka zabe ta."
"Ina da yaƙinin sun yi nazari sosai kafin saka wannan lokacin kuma shugaban ƙasa ya shirya aiwatar da kidayar yawan yan Najeriya a shekarar 2022."

A wani labarin kuma Shugaba Buhari ya dakatad da shirin rantsar da yan majalisan gudanarw na Kamfanin NNPC

A sanarwan da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya fitar, yace za'a sanar da sabuwar rana nan gaba.

Kara karanta wannan

Ba zamu taba yarda a kara farashin man fetur ba, Kungiyar Kwadago NLC

Tun a watan Satumba, Shugaban Buhari ya naɗa mashawarta a kamfanin man fetur mallakin gwamnatin tarayya NNPC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel