Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya dakatad da rantsarda shugabannin Kamfanin NNPC

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya dakatad da rantsarda shugabannin Kamfanin NNPC

  • Shugaban kasa Buhari ya bada umarnin dakatar da shirin rantsar da sabbin yan majalisar gudanarwa na kamfanin NNPC
  • A sanarwan da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya fitar, yace za'a sanar da sabuwar rana nan gaba
  • Tun a watan Satumba, Shugaban Buhari ya naɗa mashawarta a kamfanin man fetur mallakin gwamnatin tarayya NNPC

Abuja - Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bada umarnin ɗage shirin rantsar da sabbin shugabannin kamfanin man fetur na ƙasa NNPC.

Dailytrust tace shirin rantsar da su da aka tsara gudanar wa ranar Laraba, an ɗage shi har zuwa wani lokaci nan gaba.

Sai dai babu wani cikakken bayani da gwamnatin tarayya ta bayyana kan dalilin ɗage rantsar da mutanen.

Shuagaba Buhari
Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya dakatad da rantsarda shugabannin Kamfanin NNPC Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Yaushe za'a rantsar da su?

Kara karanta wannan

Ba zamu taba yarda a kara farashin man fetur ba, Kungiyar Kwadago NLC

A wata sanarwa da sakataren gwamnatin tarayya, (SGF), Boss Mustapha, ya fitar, ya bayyana cewa za'a sanar da sabuwar rana idan lokacin ya yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Vanguard ta rahoto Sakataren gwamnatin yace:

"Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin gaggawa na dakatar da rantsar da sabbin shugabannin kamfanin NNPC."
"An shirya za'a rantsar da sabbin shugabannin ranar Laraba 24 ga watan Nuwamba, amma yanzun sai an sake fitar da sanarwa."
"Bamu ji daɗin wannan matsalar da aka samu ba kuma muna dana sanin halin da mambobi zasu ji da lamarin ɗage rantsarwan."

Yaushe Buhari ya naɗa mambobin NNPC?

A ranar 19 ga watan Satumba, 2021, shugaba Buhari ya amince da naɗin sabbin waɗan da zasu jagoranci kamfanin NNPC.

Ya amince da naɗin sanata Ifeanyi Ararume a matsayin shugaba, sai kuma manajan kamfanin, Mele Kyari, a matsayin shugaban gudanarwa da dai sauransu.

Kara karanta wannan

Labari cikin Hotuna: Shugaba Buhari na jagorantar taron majalisar zartarwa FEC a Aso Villa

A wani labarin na daban kuma Gwamna Ganduje ya yi magana kan shirin gwamnatinsa na tube Shekarau daga sarautan 'Sardaunan Kano'

Gwamnatin jihar Kano ta musanta rahoton cewa gwamna Ganduje ya fara shirin tube Shekarau daga sarautar Sardauna.

Gwamnatin ta bayyana cewa wannan labarin hasashe ne kawai kuma ba shi da tushe balle makama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel