Zamu nunawa yan Najeriya cewa PDP ta canza, Gwamnan jihar Oyo

Zamu nunawa yan Najeriya cewa PDP ta canza, Gwamnan jihar Oyo

  • Jam'iyyar PDP ta shirya taro na musamman don horar da sabbin shugabanninta da ake gab da rantsarwa
  • Daya daga cikin Gwamnonin PDP ya bayyana cewa mutane sun yanke kauna a yin zabe saboda gazawar yan siyasa
  • A cewarsa, yan siyasa suna yawan alkawura amma su gaza cika alkawuran da suka yi

Abuja - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ranar Laraba ya bayyana cewa sabbin Shugabannin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP zasu nunawa yan Najeriya cewa jam'iyyar ta canza.

Makinde ya bayyana cewa wajibi ne jam'iyyar ta nunawa yan Najeriya cewa ta shirya mulkan jama'a yadda ya kamata kuma da adalci.

Ya kara da cewa akwai alaka tsakanin rashin son fitowa kada kuri'a da gazawar Shugabanni.

A jawabin da Sakataren yada labaran Gwamnan, Taiwo Adisa, ya saki, yace maigidansa ya bayyana hakan a zaman horo da aka yiwa sabbin shugabannin PDP a Abuja, rahoton Thisday.

Kara karanta wannan

Gwamnan Nasarawa: APC bata shirya faduwa a 2023 ba, muna da shiri mai kyau

Gwamnan jihar Oyo
Zamu nunawa yan Najeriya cewa PDP ta canza, Gwamnan jihar Oyo Hoto: Seyi Makinde
Asali: Twitter

A cewar Makinde, wajibi ne PDP ta shawo kan lamarin kin son fitowar mutane kada kuri'a gabanin zaben 2023.

Yace:

"Gabanin 2023, daya daga cikin manyan abubuwan da ya kamata mu nemi sauyi shine rashin son zabe da mutane ke yi kuma ba zamu iya magance matsalar nan ba ta hanyar uwar shegu da babban abin da ya haifar da hakan."
"Idan zamu fadawa juna gaskiya, mun san gazawar yan siyasa ne babban dalilin da yasa mutane suka fidda tsammani da zabe."
"Mun cika alkawura amma mu gaza cikawa mutane."

Tsohon gwamna ga PDP: Ku bar tikitin shugaban kasa a zaben 2023 ga mai rabo

Tsohon gwamnan jihar Neja, Mu’azu Babangida Aliyu, ya bayyana cewa maimakon mika tikitin shugaban kasa na 2023 ga wani yanki, kamata yayi a bude shi ga yan Najeriya da suka cancanta.

Kara karanta wannan

Shirin kidaya yawan yan Najeriya zai lakume sama da Biliyan N190bn a 2022, Majalisa

Ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana a wani shirin Daily Politics na Trust TV a ranar Laraba, 24 ga watan Nuwamba.

Aliyu ya tuna cewa ya kasance mamba a kwamitin shiya na jam'iyyar PDP wanda yayi rabon kujeru a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel