Ba zamu taba yarda a kara farashin man fetur ba, Kungiyar Kwadago NLC

Ba zamu taba yarda a kara farashin man fetur ba, Kungiyar Kwadago NLC

  • Kungiyar NLC ta yi tsokacinta na farko kan maganar kara farashin man fetur da gwamnati ke shirin yi
  • Ayuba Wabba ya bayyana cewa akwai rainin hankali cikin lamarin kuma haka ya saba yarjejeniyarsu da Gwamnati
  • Gwamnati tace idan ta kara farashin, zata rabawa yan Najeriya rarar kudin a dubu biyar-biyar a wata

Birnin tarayya Abuja - Kungiyar kwadagon Najeriya NLC ta yi Alla-wadai da shirin kara farashin man fetur da Gwamnatin tarayya ke shirin yi a sabon shekara 2022.

Shugaban NLC, Ayuba Wabba, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya baiwa manema labarai a Abuja, cewar Premium Times.

Wabba yace da ban dariya Gwamnati na kokarin maishe da yan Najeriya abin wasa ta hanyar alkawarin rabawa mutum milyan arba'in kudi N5000 don rage zafin da karin farashin zai haifar.

Kara karanta wannan

N2.3tr muka ware don rabawa yan Najeriya kayan tallafin Korona, Gwamnatin tarayya

A cewarsa:

"Yarjejniyar da Gwamnatin Najeriya tayi da jama'arta, musamman ma'aikata shine an dakatad da maganar tallafin mai har ila ma shaa'aLLahu."
"Sakamakon sabbin maganganun da muke ji tsakanin Gwamnati da kungiyoyin kasashen waje, NLC na sanar da cewa ba zata yarda da cire tallafi ba."

Shugaban NLC yace kokarin da Gwamnatin ke yi a kwatanta farashin mai a Najeriya da wasu kasashe kamar kwatanta Tuffa da Mangwaro ne.

Kungiyar Kwadago NLC
Ba zamu taba yarda da a kara farashin man fetur ba, Kungiyar Kwadago NLC

Zamu kara kudin mai, amma zamu fara baiwa yan Najeriya N5,000 kudin mota a wata: FG

Ministar kudi, kasafin kudi da shirye-shiryen kasa, Zainab Ahmad Shamsuna, ta bayyana cewa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zata cire tallafin man fetur a 2022.

Idan Gwamnati ta cire wannan tallafi, kudin man fetur zai yi tashin gwauron zabo.

Kara karanta wannan

Nan da watanni uku ku kara kudin man fetur: Bankin duniya ga Gwamnatin Najeriya

A madadin wannan tashi, Ministar kudin ta bayyana cewa Gwamnati za ta fara rabawa talakawan Najeriya dubu biyar-biyar a wata matsayin kudin mota.

Zainab ta bayyana hakan ne ranar Talata a taron kaddamar da rahoton Bankin Duniya (NDU).

Farashin mai na iya tashi N340 ga Lita a sabon shekara, GMD na NNPC

Dirakta Manaja na kamfanin NNPC, Malam Mele Kyari, ya tofa nasa albarkacin bakin kan lamarin cire tallafin man fetur a sabuwar shekarar 2022 da ake fuskanta.

A nasa jawabin, ya bayyana sabon farashin man da ake sa rai na iya konawa tsakanin N320 da N340 ga lita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel