Yadda makwabta suka kama wani mutum da ya kutsa gidan makauniya ya yi mata sata

Yadda makwabta suka kama wani mutum da ya kutsa gidan makauniya ya yi mata sata

  • An gurfanar da wani Adewale Oladeji a gaban kotu kan zarginsa da kutse gidan wata mata makauniya da yin sata
  • Mai gabatar da kara ya ce Oladeji da abokinsa sun tafi gidan matar sun sace wayar Android da kuma tsabar kudi N5,000
  • Sai dai kafin su fice matar ta gano mutane sun shigo mata gida, hakan ya sa tayi ihu makwabta suka kama Oladeji a waje

Jihar Legas - An gurfanar da wani mutum mai shekaru 39, Adewale Oladeji gaban alkalin kotun majistare a Legas kan zarginsa da kutse gidan wata makauniya don yin sata.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an tuhumarsa na kan aikata laifuka uku da suka hada hadin baki, balle gida da sata.

An kama wani mutum da ya kutsa gidan makauniya ya yi mata sata
An gurfanar da wani a kotu kan yi wa makauniya sata a gidanta. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Shi kaɗai ya san inda na ke ajiye asusun: Budurwa ta faɗa wa kotu saurayin ta ne ya sace mata kuɗi

Wanda ake zargin ya musanta tuhumar da ake masa kamar yadda ya zo a rahoton na Premium Times.

Mai gabatar da karar, Simeon Uche, ya shaida wa kotu cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 11 ga watan Nuwamba.

Ya ce an kama wanda ake zargin ne a gida mai lamba 5 Ebunoluwa St. a Afromedia a Okokomaiko a jihar Legas.

Yadda Oladeji da abokinsa suka kutsa gidan makauniyar

Mr Uche ya ce wanda ake zargin da abokin aikata laifinsa, wanda a yanzu ake nema, sun kutsa gidan Ofa Roseline Aiguh, wata makauniya.

Ya bayyana cewa wanda ake zargin da abokinsa sun hada baki domin sace kayan wacce ta yi karar, wanda a lokacin suke tunanin bata gida.

Ya ce wanda aka yi karar ya tsaya a waje yana gadi, yayin da abokin laifinsa ya kutsa gidan ya sace wayar salula ta Android da kudinta ya kai N50,000 da kuma tsabar kudi N5,000.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi nasarar kama wani hatsabibin dillalin miyagun ƙwayoyi a Jigawa

Mai gabatar da karar ya ce, a lokacin da wacce ta shigar da karar ta lura akwai wani a cikin gidan, ta kwallara ihu hakan ya janyo hankalin makwabta suka bi wanda ake zargin suka kama shi.

Ya ce abokin laifinsa, wanda ke cikin gidan ya tsere da rufin gidan, yayin da shi kuma wanda aka yi karar da ke waje yana gadi, makwabta suka kama shi.

Laifukan sun ci karo da sashi na 287, 307 da 411 na dokar masu laifi na jihar Legas ta 2015.

Alkalin kotun, Ademola Adesanya ya bada belin wanda ake zargin kan kudi N100,000 tare da mutane biyu da suka tsaya masa.

Ya daga cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 21 ga watan Janairun 2022.

Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba

A wani rahoton, wata kotun majistare ta daure wani matashi, Lekan Alaka, mai shekaru 19, watanni 3 bisa satar kujerun roba masu kimar N91,200 daga cocin Mount Zion Angelican.

Kara karanta wannan

Kano: Alƙalin Kotun Shari’ar Musulunci Ya Aike da Alhassan Yusuf Gidan Ɗan Kande Saboda Satar Kare

‘Yan sandan sun kama Alaka da laifin sata kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Alkali Olajumoke Somefun ya yanke hukunci bisa tabbatar da laifin da ya aikata bisa ruwayar Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel