Shi kaɗai ya san inda na ke ajiye asusun: Budurwa ta faɗa wa kotu saurayin ta ne ya sace mata kuɗi

Shi kaɗai ya san inda na ke ajiye asusun: Budurwa ta faɗa wa kotu saurayin ta ne ya sace mata kuɗi

  • Wata budurwa ta yi karar saurayinta a gaban wata kotun majistare da ke Legas kan zarginsa da sata
  • Budurwar ta yi ikirarin saurayinta Azubuike Omenehu ya sace mata N120,000 daga asusunta saboda shi kadai ya san inda asusun ya ke
  • Alkalin kotun ya saurari bayanin sannan ya bada belin saurayin kan kudi N50,000 ya dage cigaba da shari'ar zuwa ranar 2 ga watan Disamba

Jihar Legas - An gurfanar da wani Azubuike Omenehu mai shekaru 33, ranar Laraba a gaban Kotun Majistare da ke Legas kan sace wa budurwarsa N120,000 daga asusun ta, Guardian ta ruwaito.

Omenehu, da ke zaune a gida mai lamba 45, Makanjuola Streer, Orile Iganmu Legas na fuskantar tuhuma ce ta aikata sata da tserewa daga hannun hukuma.

Kara karanta wannan

Yadda makwabta suka kama wani mutum da ya kutsa gidan makauniya ya yi mata sata

Shi kaɗai ya san inda na ke ajiye asusun: Budurwa ta faɗa wa kotu saurayin ta ne ya sace mata kuɗi
Budurwa ta faɗa wa kotu saurayin ta ne ya sace mata kuɗin da ta tara a asusu. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Dan sanda mai gabatar da kara, Sufeta Courage Ekhueorohan, ya shaida wa kotun cewa wanda aka yi kararsa ya aikata laifin ne a ranar 3 ga watan Nuwamba a adireshin da aka ambata da farko.

Ya ce budurwar wanda aka yi karar, Mercy Nwaoga, ta jaddada cewa wanda ake zargin ne kadai ya san inda ta ajiye asusunta na katako kamar yadda ya zo a rahoton na Guardian.

Yan sanda sun kama Omenehu amma ya tsere

Ekhueorohan ya shaidawa kotun cewa an tsare Omenehu a ofishin yan sanda amma ya tsere, sai dai an sake kamo shi.

Ya ce laifin da ake zargin an aikata ya saba wa sashi na 106(b) da 287 na dokar masu laifi na jihar Legas ta shekarar 2015.

Kara karanta wannan

Budurwa ta fasa kwalba ta caka wa direban motar haya saboda kudin mota a Legas

Alkalin kotun, Mrs Sadiq Bello ta bada belin wanda ake zargin kan kudi N50,000 tare da mutum daya tsayayye wanda zai karbe shi.

Kotun ta saka ranar 2 ga watan Disambar 2021 domin cigaba da sauraron shari'ar.

Kano: Mata ta garzaya kotun shari'a ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda murguɗa baki

A wani labarin, mata ta maka mijin ta gaban kotu don bukatar a raba auren su sakamakon yadda rikici da tashin hankali ke aukuwa tsakanin su.

Ta bayyana gaban Alkali Munzali Tanko na kotun musulunci da ke zama a Kofar Kudu a birnin Kano don gabatar da korafin ta bisa ruwayar Dala FM.

Kamar yadda ta ce, mijin na ta ya na ci wa iyayen ta mutunci kuma ba ya ganin darajar su ko kadan kamar yadda ya zo a ruwayar na Dala FM.

Asali: Legit.ng

Online view pixel