'Yan sanda sun yi nasarar kama wani hatsabibin dillalin miyagun ƙwayoyi a Jigawa

'Yan sanda sun yi nasarar kama wani hatsabibin dillalin miyagun ƙwayoyi a Jigawa

  • Yan sanda a jihar Jigawa sun kama wani dillalin miyagun kwayoyi a karamar hukumar Hadejia
  • Yan sandan sun kama mutum mai shekaru 48 ne yayin da suke sintiri a ranar 15 ga watan Nuwamba a Gundun Quatars
  • Bayan kama shi, an kwace wasu kwallabe guda 43 dauke da wasu ababe da ake kyautata zaton miyagun kwayoyi ne

Jihar Jigawa - Rundunar 'yan sandan Nigeria, a Jigawa ta yi nasarar kama wani mutum mai shekaru 48 da ake zargin hatsabibin dillalin miyagun kwayoyi ne.

An kama shi ne a karamar hukumar Hadejia da ke jihar ta Jigawa kamar yadda ya zo a ruwayar The Nation.

'Yan sanda sun yi nasarar kama wani hatsabibin dillalin miyagun ƙwayoyi a Jigawa
An kama wani hatsabibin dillalin miyagun ƙwayoyi a Jigawa. Hoto: The Nation
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta rahoto cewa ASP Lawan Shiisu, mai magana da yawun rundunar yan sandan Jigawa, ne ya sanar da hakan a ranar Juma'a a Dutse, babban birnin jihar.

Read also

An damke mutane 15 da suka kashe babban jami'in dan sanda

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda aka kama wanda ake zargin

Shiisu ya ce tawagar wasu 'yan sanda ne suka kama wanda ake zargin a ranar 15 ga watan Nuwamba misalin karfe 12.30 na rana.

Ya yi bayanin cewa tawagar, yayin da suke sintiri a Hadejia sun kama wanda ake zargin a Gundun Sarki Quaters.

Abin da aka kwace a hannunsa

Kakakin yan sandan ya kara da cewa an samu kwallabe 43 na wasu abubuwa da ake zargin muggan kwayoyi ne a hannun wanda ake zargin.

Ya ce za a gurfanar da shi a gaban kotu idan an kammala bincike.

Shiisu ya kara da cewa an kama wasu mutane shida da ake zargin bata gari ne a karamar hukumar Kiyawa.

Ya ce an kama su ne bayan kai samame a mabuyar bata gari da kauyen Balago a ranar 16 ga watan Nuwamba misalin karfe 7 na yamma.

Read also

Ango a hannun hukuma: ‘Yan sanda sun yi ram da dan fashi ta hanyar bin diddigin fostar aurensa

Da an kammala bincike suma za a gurfanar da su a kotu.

'Yan sanda sun yi ram da wasu samari 2 bayan sun datse wa juna hannaye yayin kwasar dambe

A wani labarin, 'yan sanda sun yi ram da samari 2 bisa kama su dumu-dumu da laifin sare wa juna hannaye, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

An ruwaito yadda ‘yan sandan su ka kama Adamu Mohammed da Bukar Audu, bayan sun datse wa juna hannaye yayin wani fada da su ka tafka a Garin Alkali, karamar hukumar Dapchi da ke jihar Yobe.

Premium Times ta bayyana yadda Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, a ranar Litinin a Damaturu ya bayyana a wata takarda.

Source: Legit

Online view pixel