Matar aure: Abin da yasa na yi garkuwa da kai na, na nemi miji na ya biya N50,000

Matar aure: Abin da yasa na yi garkuwa da kai na, na nemi miji na ya biya N50,000

  • Wata matar aure a Ekiti ta yi bayani dalla-dalla akan dalilinta na shirya makircin garkuwa da kanta da kanta
  • Bayan rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti sun kama matar sun gano cewa da kanta ta shirya makircin
  • Sai dai an gano cewa matar mai suna Sule ta bukaci mijinta ya warwaro naira dubu hamsin a matsayin kudin fansa

Jihar Ekiti - Rundunar ‘yan sandan jihar sun yi ram da wata mata, Sule ‘yar asalin jihar bisa tafka makircin garkuwa da kanta da kanta kamar yadda Tribune ta ruwaito.

An gano yadda ta shirya garkuwa da kanta da kuma babban dalilin da ya tunzurata ta aikata hakan.

Matar aure: Abin da yasa na yi garkuwa da kai na, na nemi miji na ya biya N50,000
Matar aure ta yi garkuwa da kanta ta nemi mijinta ya biya N50,000 kudin fansa. Hoto: The Nation

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Masu garkuwa sun kashe tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Kamar yadda aka tabbatar masu garkuwa da matar sun bukaci naira dubu hamsin daga hannun mijinta a matsayin kudin fansa.

Tuni ‘yan sanda suka wuce da matar da wadanda ta hada kai aka tafka laifin zuwa Ado-Ekiti, babban birnin jihar a ranar Laraba.

Rundunar RRS ne suka kama matar da abokan harkar nata

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Sunday Abutu ya ce Rapid Respond Squad ne suka kama su bayan yin bincike mai yawa akan lamarin.

Ya yi bayani akan yadda lamarin ya faru a ranar Asabar lokacin da aka kira mijinta cewa an yi garkuwa da matarsa a kan titin Ifaki zuwa Oye Ekiti.

Abutu ya kara da cewa matar ta kara kira inda take cewa masu garkuwa da mutanen sun bukaci N50,000 a matsayin kudin fansa kafin a sake ta.

A cewar Kakakin:

“Jami’an RRS, bayan kai musu rahoto, sun fara bincike dazukan da ke wuraren Ofaki zuwa Oye-Ekiti kafin a gano cewa ita ta yi garkuwa da kanta don samun kudi daga ‘yan uwanta."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace dan uwan hadimin Jonathan da wasu mutum 8 a Kwara

Ina bukatar kudi ne shi yasa na yi garkuwa da kai na, matar auren

A cewarta:

“Ina bukatar wasu kudi amma bana da mataimaki don haka na yanke shawarar garkuwa da kaina don in amshi N50,000 daga hannun mijina daga nan aka kama ni.”

Sai dai ‘yan sandan sun kama wasu mutane biyu cikin wadanda suka hada kai da ita wurin garkuwa da matar, ciki har da wani korarren soja, wanda aka gano sunansa Samuel.

Ana zargin su na da hannu a garkuwa da mutane har da fashi da makamai da ake yi a cikin jihar da kewaye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel