EFCC ta gurfanar da mataimakin ma'ajin jami'ar ABU kan zargin wawurar N6m

EFCC ta gurfanar da mataimakin ma'ajin jami'ar ABU kan zargin wawurar N6m

  • Hukumar EFCC reshen jihar Kaduna a ranar Talata ya gurfanar da mataimakin ma’ajin jami’ar Ahmadu Bello, Iliyasu Abdulrauf Bello gaban kotu
  • Hukumar ta gurfanar da shi gaban alkalin babbar kotun jiha da ke zama a Kaduna, Justice Darius Khobo bisa zarginsa da amsar cin hancin N6,000,000
  • Iliyasu ne mukaddashin shugaban kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya reshen jami’ar, SSANU, an zargeshi da amfani da matsayinsa wurin wawurar kudin kungiya

Kaduna - Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta gurfanar da mataimakin ma’ajin jami’ar Ahmadu Bello, Iliyasu Abdulrauf Bello gaban alkali Darius Khobo na babbar kotun jihar Kaduna bisa zarginsa da kwasar N6,000,000.

Iliyasu na rike da kujerar mukaddashin shugaban kungiyar manyan ma’aikatan jami’ar, SSANU, reshen jami’ar. Ana zarginsa da wawurar wasu kudade daga asusun kungiyar da aka ware don walwalar ma’aikatan.

Kara karanta wannan

Buni ya bayyana dalilai 5 da suka sanya Buhari kai babban taron APC watan Fabrairun 2022

EFCC ta gurfanar da mataimakin ma'ajin jami'ar ABU kan zargin wawurar N6m
EFCC ta gurfanar da mataimakin ma'ajin jami'ar ABU kan zargin wawurar N6m. Hoto daga Economic and Financial Crime Commission
Asali: Facebook

Bincike ya nuna yadda aka dinga wawurar kudade daga cikin asusun kungiyar ba tare da mambobin kungiyar sun sani ba.

Takardar da aka gabatar gaban kotun ta bayyana kamar haka:

“Cewa kai Ilyasu Abdulrauf Bello a wani lokaci cikin Disamban 2018 a cikin Kaduna a matsayin ka na mukaddashin shugaban SSANU reshen ABU, ka wuwuri N6,325,000.00 daga gaba daya kudaden da aka ware wa SSANU reshen ABU.
" Ka cire N6,825,000 ga kamfanin P.A NDAHI don hatimi a jikin riguna da huluna (Hana-Sallah). Don haka ka aikata laifin da ya ci karo da sashi na 19 na laifukan rashawa da makamantansu na 2000, kuma hukuncin ya na karkashin wannan sashin.”

Sai dai bai amsa laifin nasa ba sannan lauyan masu kara, J. Musa ya bukaci kotu ta sanya ranar ci gaba da shari’ar yayin da lauyan wanda ake kara, J. H Dacep ya bukaci kotu ta amince da belin wanda yake karewa.

Kara karanta wannan

2023: Saraki ya ziyarci wata jihar arewa kan kudirinsa na son hayewa kujerar Buhari

Alkali Darius Khobo ya amince da bayar da belin mai laifin da N2,000,000 da kuma tsayayye wanda wajibi ne ya zama mazaunin Zaria kuma yana da wani fili mai takarda a garin.

Alkalin ya bayar da umarnin cewa magatakardan kotun da hukumar su tantance tsayayyen.

EFCC ta sake gurfanar da dan uwan Saraki da tsohon kwamishinan Kwara

A wani labari na daban, hukumar yaki da rashawa ta EFCC reshen jihar Ilori, a ranar Litinin ta gurfanar da Ope Saraki, dan’uwan tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da kuma tsohon kwamishinan labarai na jihar Kwara, Olatunji Oyeyemi Moronfoye a gaban kotu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, hakan ya biyo bayan zarginsu da amfani da ofishinsu ta hanyar da bai dace ba, yasar kudin al’umma da halasta kudin haram.

Zasu tsaya gaban alkali Muhammed Sani na babbar kotun tarayya dake zama a Ilori, Daily Trust ta ruwaito.

Dama an fara shari’ar ne tun ranar 13 ga watan Mayun 2015 a gaban Alkali Olayinka Faji na babbar kotun tarayya da ke Ilorin ne, inda aka dinga samun koma baya saboda canje-canjen alkalai.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki: Jam’iyyar PDP ta sake rashi na wani babban jigonta

Asali: Legit.ng

Online view pixel