Abun bakin ciki: Jam’iyyar PDP ta sake rashi na wani babban jigonta

Abun bakin ciki: Jam’iyyar PDP ta sake rashi na wani babban jigonta

  • Babban jigon jam'iyyar PDP a karamar hukumar Ughelli ta arewa da ke jihar Delta, Cif Lawrence Agbatutu, ya mutu
  • Kakakin Gwamna Ifeanyi Okowa ne ya sanar da labarin mutuwarsa a ranar Litinin, 22 ga watan Nuwamba
  • Zuwa yanzu jam'iyyar adawar kasar bata fitar da wani bayani ba game da mutuwar jigon nata a hukumance

Jihar Delta - Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta sake rashi na wani jigonta a jihar Delta, Cif Lawrence Agbatutu.

Har zuwa mutuwarsa, marigayin ya kasance shugaban PDP a karamar hukumar Ughelli ta arewa da ke jihar.

Abun bakin ciki: Jam’iyyar PDP ta sake rashi na wani babban jigonta
Abun bakin ciki: Jam’iyyar PDP ta sake rashi na wani babban jigonta Hoto: Ovie Success Ossai
Asali: Facebook

Ovie Success Ossai, daya daga cikin hadiman Gwamna Ifeanyi Okowa, ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook a safiyar ranar Litinin, 22 ga watan Nuwamba.

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Gaba da gaban ta: Bidiyo da hotunan Tinubu ya na jinjina, gurfane gaban Aminu Dantata

“Yanzun nan muka rasa shugaban PDP a karamar hukumar Ughelli ta arewa, Hon. Lawrence Agbatutu. Allah ya ji kansa.”

Yan kwanakin baya, wani dan takarar gwamna kuma tsohon kwamishinan tattalin arziki a karkashin gwamnatin Dr Emmanuel Uduaghan, Cif Kenneth Okpara, ya mutu.

Kafin nan, mambobin majalisar jihar Delta biyu daga Isoko ta arewa da kudu sun mutu a farkon shekarar nan.

Hadimar Okowa, Mary Iyasere itama ta mutu yan makonnin da suka gabata a Delta.

A halin da ake ciki, ana sauraron jin rahoton mutuwar a hukumance daga iyalan marigayin.

Ni da mahaifiyata muna kallo lokacin da aka zare ran kanina amma babu yadda muka iya - Dangote

A wani labarin, mun kawo a baya cewa mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote, ya magantu a kan rasuwar kaninsa, Alhaji Sani Dangote.

Marigayin wanda ya kasance mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Dangote, ya rasu a ranar Lahadi, 14 ga watan Nuwamba, a kasar Amurka bayan ya yi jinya.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi a jihar Nasarawa kan kisan wasu makiyaya

Da ya tarbi jagoran jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a gidansa da ke Kano, a ranar Juma'a, 19 ga watan Nuwamba, Dangote ya ce mahaifiyarsu da yaran Sani na a wajen da aka dauki ran marigayin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel