Gyaran tarbiyya: Jami'ar Dutse ta haramtawa dalibai mata yin hira da daddare

Gyaran tarbiyya: Jami'ar Dutse ta haramtawa dalibai mata yin hira da daddare

  • A kokarinta na kula da tarbiyya, jami'ar tarayya ta Dutse, jihar Jigawa ta haramta ziyarar dalibai mata da daddare
  • Hakazalika shugaban jami'ar ta FUD, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed ya hana samari shiga makarantar da motoci masu bakin gilashi
  • Ya kuma bukaci masu ikirarin su za su auri daliban da su dunga zuwa gidajensu yin hira amma ba wai a makaranta da daddare cikin mota ba

Jihar Jigawa - Shugaban jami'ar tarayya ta Dutse, jihar Jigawa, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed ya haramtawa samari masu yawon dare ziyarar jami'ar.

Da yake magana a wani shirin radiyo a garin Dutse, shugaban makarantar ya ce dalibai mata sun zo jami'ar ne domin yin karatu kuma masu kula da su, hukumar jami'ar ba za su bari wasu bata-gari su lalata masu tarbiya ba.

Kara karanta wannan

Matar Obasanjo ta shawarci mata: Kada ku tsammanci neman afuwa daga mazajenku

Gyaran tarbiyya: Jami'ar Dutse ta haramtawa dalibai mata yin hira da daddare
Gyaran tarbiyya: Jami'ar Dutse ta haramtawa dalibai mata yin hira da daddare hOTO: NewsWireNGR
Asali: UGC

Ya ce an kai karar dalibai mata da aka gani suna aikata ba daidai ba a yayin fatrol din dare ga iyayensu, rahoton Daily Trust.

Mohammed ya ce a wannan karni na rashin tsaro, musamman garkuwa da mutane, jami'ar ba za ta lamunci motoci masu bakin gilashi ba da rana da kuma dare.

Shugaban makarantar ya ce wadanda ke ikirarin cewa sune wadanda za su auri daliban mata toh su dunga kai masu ziyara a gidajensu amma ba wai a jami'ar ba da daddare cikin motoci masu bakin gilashi.

Ya kuma yi gargadin cewa daga yanzu duk wanda aka kama da aikata hakan, toh zai fuskanci hukunci.

Ya kuma gargadi malamai da sauran ma'aikata a kan cin zarafin dalibai ta hanyar lalata sannan ya gargadi daliban da su guji dabi'u marasa kyau ga ma'aikatan jami'ar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Masu garkuwa sun kashe tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Ya bayyana cewa shirin jagoranci na jami'ar ya fara. A karkashin shirin, za a jona kowani dalibi da malamia matsayin masu ba da shawara wadanda za su kasance masu kula da su a duk tsawon zamansu a jami'ar.

Ya kuma kara da cewa ana sa ran malaman za su ba wa dalibai shawara ta bangaren ilimi, dabi'a da zamantakewa da sauransu.

Farfesa Mohammed ya kuma ce jami'ar ba za ta lamunci ta'ammali da miyagun kwayoyi ba sannan duk dalibin da aka kama zai fuskanci doka.

Jaridar Tribune ta kuma rahoto cewa jami’ar ta Dutse ta dauki hayar mafarauta 55 na gida domin inganta tsaro a cikin harabar makarantar da kewaye.

Babban jami’in yada labarai na makarantar, Alhaji Abdullahi Yahaya ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Dutse, babban birnin jihar a ranar Talata.

Yahaya ya ce shugaban jami’ar, Farfesa Abdulkarim Sabo, ya amince da daukar mafarautan.

Kara karanta wannan

Kafa Ƙasar Biafra Da Oduduwa: Tsohon Mai Neman Takarar Shugaban Ƙasa Daga Arewa Ya Goyi Bayan Kanu da Igboho

Jami'ar Ilorin ta kori dalibin dan aji hudu da ya lakadawa lakcararsa dukan kawo wuka

A wani labari na daban, hukumar gudanarwar jami’ar Ilorin ta kori wani dalibi mai suna Salaudeen Waliu Aanuoluwa na tsangayar nazarin ilmin halittu, bayan da aka same shi da laifin cin zarafin wata malamar jami’ar, Misis Rahmat Zakariyau.

A baya mun kawo muku rahoton yadda dalibin jami'ar dan aji hudu ya lakadawa lakcararsa dukan kawo wuka a harabar jami'ar saboda kin taimakonsa.

Wata sanarwa da Daraktan hulda na Jami’ar, Mista Kunle Akogun, ya fitar, ta bayyana cewa kwamitin ladabtarwa na dalibai ne ya yanke hukuncin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel