Matar Obasanjo ta shawarci mata: Kada ku tsammanci neman afuwa daga mazajenku

Matar Obasanjo ta shawarci mata: Kada ku tsammanci neman afuwa daga mazajenku

  • Uwargidar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ta shawarci mata kan yadda za su rike gidajen aurensu
  • Aduke Obasanjo ta ce ba daidai bane mace ta tsammaci ban hakuri daga mijinta koda kuwa shi ke da laifi
  • Ta ce don mace na daukar dawainiyar gida ta bangaren kudi wannan bai bata lasisin raina mijinta ba

Jihar Lagas - Aduke Obasanjo, uwargidar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ta ce ba daidai bane ga mata su tsammaci ban hakuri daga mazajensu koda kuwa mazan ne ke da laifi.

Ta yi magana ne a ranar Lahadi, a wani taro da aka yi a hedkwatar cocin Celestial Church of Christ da ke Ketu, jihar Lagas, rahoton Punch.

Read also

Abuja: Yadda sojoji suka lakaɗa wa basarake dukan kawo wuka tare da iyalansa

Matar Obasanjo ta shawarci mata: Kada ku tsammanci neman afuwa daga mazajenku
Matar Obasanjo ta shawarci mata: Kada ku tsammanci neman afuwa daga mazajenku Hoto: Olusegun Obasanjo
Source: Facebook

Misis Obasanjo, wacce ta wakilci mijinta a taron da kuma shawartan mata kan yadda za su gyara gidajensu, ta gargade su kan bude sirrin gidajen aurensu ga bare.

Yayin da take cewa martaba ne ga mace daukar sunar matar aure, ta bukaci matan da ke daukar dawainiyar iyalinsu ta bangaren kudi da kada su raina mazajensu, ruwayar Daily Trust.

Aduke ta ce:

“Allah ne ya albarkaci matan da ke daukar dawainiyar mazajensu; wannan bai isa dalili da zai sa su raina mazajen nasu ba.
“Maimakon sanya ran namiji ya bayar da hakuri, kamata yayi ace mata su koyi yadda za su jagoranci mazajensu zuwa dakin baccinsu sannan su shafa su cikin kissa. Duk abun da kuka yi a gidajen ku zai yi tasiri a kan yara kuma wadannan yaran sune tushen kwanciyar hankalinku. Kwanciyar hankalin da kika ba mijinki yana da matukar muhimmanci.”

Read also

Da Duminsa: Masu garkuwa sun kashe tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a hanyar Abuja zuwa Kaduna

'Yar Sarkin Kano Sanusi: Na gwammace ɓarawo ya sace kuɗin da in bawa miji na N500,000 ya ƙara aure

A wani labarin, Shahida, yar Sarkin Kano na 14, Sanusi Lamido Sanusi, tace ta gwammace barayi su sace mata N500,000 a maimakon ta bawa mijinta kudin ya kara cikin gara domin auro mata kishiya.

Mahaifiyar 'ya'ya biyun ta bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 21 ga watan Nuwamban 2021, yayin da ta ke martani kan wata wallafa da aka yi a shafin Instagram.

Wallafar ya ce:

"Wannan na mata ne. Kina da N500k, za ki bawa mijin ki a matsayin gudunmawa domin ya kara mata ta biyu ko kuma kin gwammace a sace kudin"

Source: Legit

Online view pixel