Ganduje ya yi magana kan shirin gwamnatinsa na tube Shekarau daga Sarautan 'Sardaunan Kano'

Ganduje ya yi magana kan shirin gwamnatinsa na tube Shekarau daga Sarautan 'Sardaunan Kano'

  • Gwamnatin jihar Kano ta musanta rahoton cewa gwamna Ganduje ya fara shirin tube Shekarau daga sarautar Sardauna
  • Gwamnatin ta bayyana cewa wannan labarin hasashe ne kawai kuma ba shi da tushe balle makama
  • A cewar hadimin gwamnan, Ganduje mutum ne dake saka sharri da alkairai masu yawa

Kano - Gwamnatin jihar Ƙano, ta musanta rahoton cewa gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya fara shirin tube Shekarau daga mukamin sarauta na 'Sardaunan Kano'

Tribune Online tace Gwamnatin ta kira raɗe-radin da mutane ke yaɗawa da mara amfani kuma mara tushe ballantana makama.

Idan baku manta ba, manyan jiga-jigan APC biyu sun fara taƙaddama da juna a lokacin gangamin taron jam'iyya na jihar Kano.

Ganduje da Shekarau
Rikicik APC a Kano: Gwamna Ganduje ya yi magana kan shirin gwamnatinsa na tube Shekarau daga 'Sardaunan Kano' Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton yadda kowane tsagi tsakanin gwamna Ganduje, da Sanata Ibrahim Shekarau ya fitar da shugaban APC a matakin jiha.

Kara karanta wannan

Gaba da gaban ta: Bidiyo da hotunan Tinubu ya na jinjina, gurfane gaban Aminu Dantata

Yayin da tsagin gwamna Ganduje ya zaɓi Abdullahi Abbas a matsayin shugaba, shi kuma Shekarau ya bayyana Alhaji Haruna Danzago a matsyain shugaba.

Waya naɗa Shekarau Sardauna?

Marigayi Sarki Ado Bayero, shine ya naɗa Malam Ibrahim Shekarau sarautar Sardaunan Kano, a shekarar 2007, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Sai dai jita-jita ta fara yawo cewa gwamnan Kano na yanzun ya fara shirin yadda za'ayi a tube wannan rawanin daga kan Shekarau.

Wane martani gwamnatin Kano ta yi?

Da yake martani kan jita-jitan, babban hadimin Ganduje kan harkokin naɗe-naɗen Sarauta, Alhaji Tijjani Mailafiya Sanka, yace:

"Labarin da ake yaɗawa ba wani abu bane hasashe ne wanda bashi da tushe. Ganduje na kowa ne, ba ya aje mutum a zuci, kuma mutum ne dake saka sharri da alkairai da yawa."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APGA ta yi magana kan shirin sauya shekar Gwamnan Anambra, Obiano da Saludo zuwa APC

"Lokacin da siyasa ta juya wa Shekarau baya a 2019, Ganduje ne ya ɗakko shi ya hana kowa ya nemi Sanatan Kano ta tsakiya sai shi."
"Gwamna ya yi haka ne da zuciya ɗaya, duk da sun kasance masu adawa da juna a gwamnati tun daga 2003 zuwa 2015. Amma Ganduje mutum ne dake aje komai a gefe, ya rumgumi Shekarau ya nemi Sanata."

A wani labarin kuma wani Basarake ya gwangwaje diyarsa da kyautar mota bayan ta kammala digiri da daraja ta farko

Diyar Sarkin, Gimbiya Zainab Adebunmi Adeyemi, ta kammala karatun digiri da sakamako mafi girma, ta samu kyautar mota.

Hotunan motar da suka watsu a kafafen sada zumunta ya jawo cece-kuce daga bakin mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel