Minista Pantami ya jero dalilai 5 da suke nuna Najeriya a shirye take a bangare kasuwanci

Minista Pantami ya jero dalilai 5 da suke nuna Najeriya a shirye take a bangare kasuwanci

  • Isa Pantami, ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, ya ce Najeriya ce kasuwar da ta fi dacewa ta bangaren zuba jari
  • A cewarsa, Allah ya albarkaci kasar kuma tana da duk wani abu da kowani mai hannun jari ke bukata don bunkasa kasuwancinsu
  • Ya kuma yarda cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na samar yanayi don saukaka kasuwanci

An bayyana Najeriya a matsayin kasa mai albarka da tarin damammaki ga kowa domin bunkasa kasuwancinsu.

Isa Pantami, ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani ne ya bayyana hakan yayin da yake magana a tashar NTA a matsayin bako.

Minista Pantami ya jero dalilai 5 da suke nuna Najeriya a shirye take a bangare kasuwanci
Minista Pantami ya jero dalilai 5 da suke nuna Najeriya a shirye take a bangaren kasuwanci Hoto: peeterv
Asali: Getty Images

Ya kuma bayyana cewa kusancin da kasar ke da shi da nahiyar Afrika ta tsakiya ya samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari na waje duk da matsalolin rashin tsaro.

Kara karanta wannan

Aisha Yesufu ga majalisar dokoki: Ku tsige Buhari, har 'yan Arewa sai sun ji dadin haka

Kalaman Pantami:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mun samu damar nuna masu nasarar da muka samu zuwa yanzu ta bangaren tsaro, idan aka zo kan ababen more rayuwa, kamar a bangarena da wasu da dama.
“Wadannan sune wasu daga cikin nasarorin da muka samu a lokacin taron hadin gwiwar Najeriya da kasashen duniya wanda a ganina wani ci gaba ne na samun damar janyo masu zuba jari zuwa Najeriya.
“Mun samu damar yi masu bayani kan kokarin da gwamnati tayi zuwa yanzu da kuma yanayin da aka samar; kasuwar da muke da shi. Najeriya na da tattalin arziki mafi girma a Afrika kuma ta kasance kasa mafi shahara a Afrika.
“Allah ya albarkace mu da matasa da suka fahimci fasaha kuma a lokaci guda, mun nuna masu cewa zuwa Najeriya don zuba jari a bangaren tattalin arzikin zamani kamar mamaye nahiyar Afrika gaba daya ne, fara daga Yammaci zuwa Afrika ta tsakiya.”

Kara karanta wannan

Labari da Hotuna: Yadda mata zasu iya taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya, Shugaba Buhari

Ministan ya ci gaba da bayanin cewa Najeriya na da yawan mutane da suka kai sama da miliyan 200 kuma Najeriya ce ke da mafi yawan al’umma a Afrika.

Ya ci gaba da cewa:

“Don haka, idan ka zuba jari a Najeriya, kana damar isa ga mutane sama da miliyan 200 a cikin kasar kuma kana hanyar isa ga Yammacin Afrika inda kake da karin mutane miliyan 200 da karin mutane miliyan 150 a Afrika ta tsakiya.
“Idan ka hada Najeriya da Yammacin Afrika da Afrika ta tsakiya, za isa ga mutane miliyan 550. Idan ka duba yanayin kasar Najeriya, tana a cibiyar Afrika ne. Da wannan, za ka isa ga kimanin mutane biliyan 1.3 a Afrika.
“Mun samu damar nuna masu yanayi mai kyau, kasuwar da muke da shi a Najeriya da kuma damar mamaye Yammacin Afrika a bangare daya da kuma Afrika ta tsakiya a daya bangaren da damar bunkasa kasuwancinka zuwa sauran kasashen Afrika daga Najeriya, wacce ke a cibiyar Afrika.”

Kara karanta wannan

Tinubu ya bayyana dalilin da yasa ya ziyarci Orji Kalu a Abuja

Pantami ya yarda cewa da wadannan abubuwa da aka ambata a baya, Najeriya ce wurin da ya fi dacewa don zuba hannun jari inda ya fada ma masu zuba jari da su yi amfani da wannan damar.

Nan gaba kadan Najeriya zata shiga sahun kasashen duniya mafi karfin tattalin arzikin zamani, Sheikh Pantami

A wani labarin, Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami, yace bada jimawa tattalin arzikin zamani zai shiga sahun mafi karfi a duniya.

The Cable ta rahoto cewa Ministan ya yi wannan furucin ne a wurin taro karo na biyu a tsangayar kimiyya da fasaha ta kwalejin fasaha dake Bauchi.

Pantami yace taken taron, 'Rawar kimiyya da fasaha da kirkire-kirekire a tattalin arzikin zamani: Domim kawo cigaba mai ɗorewa' ya na da alaƙa da manufar tattalin arzikin zamani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel