Aisha Yesufu ga majalisar dokoki: Ku tsige Buhari, har 'yan Arewa sai sun ji dadin haka

Aisha Yesufu ga majalisar dokoki: Ku tsige Buhari, har 'yan Arewa sai sun ji dadin haka

  • Aisha Yesufu ta kalubalanci majalisar dokokin Najeriya da cewa ya kamata su tsige shugaba Buhari kawai
  • Ta bayyana haka ne yayin da take martani kan harin da aka kai kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a makon nan
  • Ta bayyana cewa, har 'yan Arewa sai sun ji dadi idan 'yan majalisun suka hadu suka tsige shugaba Buhari

Kaduna - ‘Yar gwagwarmayar kare hakkin bil’adama, Aisha Yesufu, ta ce lokaci ya yi da majalisar dokokin kasar nan za ta tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari, SaharaReporters ta ruwaito.

Yesufu, wacce ita ce ta kirkiri tafiyar #BringBackOurGirls, tana mayar da martani ne kan sabon lamarin da ya faru na sace-sacen mutane da kashe-kashe a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

'Yar gwagwarmaya Aisha Yesufu
Aisha Yesufu ga sanatoci: Ku sauke Buhari, har 'yan Arewa sai sun ji dadin haka | Hoto: thecable.ng
Asali: Facebook

Ta rubuta cewa:

"Tun da naji labarin harin da kashe-kashen da aka yi a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, ban iya yin komai ba, kuma ina da wa'adi da yawa da zan cika.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun gargadi Buhari kan yi wa Nnamdi Kanu afuwa, sun bada dalilinsu

“Me Majalisar Dokoki ta Kasa take yi? A tsige Buhari! Jama'ar Arewa za su gode muku! Ba su da lafiya kuma sun gaji da mara zuciya kuma maratausayi yana bayyana a matsayin babban kwamandan tsaro.”

Martanin El-Rufa'i

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai shi ma ya yi martani kan harin da ‘yan bindiga suka kai kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda aka yi garkuwa da mutane da dama a ranar Lahadi.

Gwamnan yayi magana ne a ranar Litinin ta bakin kwamishinan tsaro na cikin gida na jihar, Samuel Aruwan.

Ya tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun kashe mutum daya tare da yin awon gaba da wasu matafiya yayin harin.

A wata sanarwa da Aruwan ya fitar ya ce an kubutar da mutum 11 daga cikin mutanen da aka sace.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace dan uwan hadimin Jonathan da wasu mutum 8 a Kwara

Ya kuma ce wadanda aka kashe yayin harin su ne shugaban makarantar Famaks British School da kuma tsohon dan takarar gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Sagir Hamidu, kamar yadda Guardian ta ruwaito.

Titin Abuja zuwa Kaduna wuri ne da ake yawan samun hare-haren ‘yan bindiga.

An ritsa da uwa da matar kasurgumin dan bindiga, Bokkolo, yayin luguden wuta a Sokoto

A wani labarin, mata da mahaifiyar Bokkolo, hatsabibin dan bindiga suna cikin gidansa a yayin da jiragen yakin sojojin saman Nigeria suka yi luguden wuta a gidansa da ke Sokoto.

Daily Trust ta rahoto cewa jiragen yakin sun halaka yan bindiga da dama da 'yan uwansu.

Wani mazaunin unguwar wanda ya tabbatar da luguden wutan a gidan Bokkolo ya ce an kashe kwamandojinsa da dama a gidan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel