Da Dumi-Dumi: Tsagerun yan bindiga sun ƙone caji ofis na yan sanda, sun hallaka jami'i a bakin aiki

Da Dumi-Dumi: Tsagerun yan bindiga sun ƙone caji ofis na yan sanda, sun hallaka jami'i a bakin aiki

  • Wasu yan bindiga da ba'a gano ko suwaye ba sun hallaka jami'in dan sanda a bakin aiki a wani harin tsakar dare a jihar Imo
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kone hedkwatar yan sanda dake Arondizuogu yayin harin na ranar Talata
  • Kwamishinan yan sandan jihar, Rabiu Hussaini, ya bada umarnin kaddamar da bincike kan lamarin cikin gaggawa

Imo- Wasu yan bindiga sun kai hari tare da ƙona hedkwatar yan sanda dake Arondizuogu a karamar hukumar Ideato, jihar Imo.

Punch ta ruwaito cewa harin wanda ya auku da misalin karfe 2:00 na tsakar daren ranar Talata, ya yi sanadin mutuwar daya daga cikin yan sandan dake bakin aiki.

Wata majiya daga yankin ta tabbatar da cewa harin ya bar ofishin yan sandan a kone bayan maharan sun gudanar da mummunan nufin su.

Kara karanta wannan

Dubun wani jagoran yan bindiga da wasu mutum hudu ya cika a jihar Neja

Hari kan yan sanda
Da Dumi-Dumi: Tsagerun yan bindiga sun ƙone caji ofis na yan sanda, sun hallaka jami'i a bakin aiki Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru

Bugu da ƙari, rahoto ya nuna cewa maharan sun yi kaca- kaca da wata motar Sienna da ake tsammanin ta DPO na ofishin ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutumin, wanda ya nemi a ɓoye sunansa yace:

"Wasu miyagun yan bindiga sun farmaki hedkwatar yan sanda dake Arondizuogu, sun ƙone ta kuma sun kashe wani jami'in ɗan sanda dake bakin aiki."
"Harin ya yi sanadin fasa kan DPO na ofishin, sun yanke shi da wuka kuma suka kona motar sa ta hawa. Sannan sun lalata wata motar Sienna dake ofishin."

Wane mataki hukumar yan sanda ta ɗauka?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar, Micheal Abattam, ya tabbatar da faruwar lamarin a wani sakon karta kwana da ya aike wa wakilin mu.

Kazalika ya ƙara da cewa tuni kwamishinan yan sandan jihar, Rabiu Hussaini, ya bada umarnin gudanar da bincike kan harin.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Miyagun yan bindiga sun kai sabon hari jihar Shugaba Buhari, sun kashe mutane da dama

Dailytrust ta rahoto Kakakin yan sanda ya rubuta a sakon cewa:

"Kwamishinan yan sandan jihar yana kan hanyar zuwa wurin da aka kai harin domin gane wa idon sa."

A wani labarin na daban kuma Jirgin yakin sojojin NAF ya yi luguden wuta kan masu karban haraji na kungiyar ISWAP a Borno

Jirgin yakin rundunar sojin sama NAF na Operation Haɗin Kai sun aika dandazon mayakan ISWAP Lahira a Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa sojin sun gano tawagar masu karban haraji hannun mutane, inda suka sakar musu ruwan bama-bamai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel