Da Duminsa: Miyagun yan bindiga sun kai sabon hari jihar Shugaba Buhari, sun kashe mutane da dama

Da Duminsa: Miyagun yan bindiga sun kai sabon hari jihar Shugaba Buhari, sun kashe mutane da dama

  • Tawagar yan bindiga a kan dandazon mashin sun farmaki kauyen Barawa dake cikin wani yanki a jihar Katsina ranar Lahadi
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun kwashe fiye da mintuna 90 suna aikata ta'adin su, inda suka kashe mutum 4
  • Jihar Katsina da shugaban kasa Buhari ya fito, na ɗaya daga cikin jihohin da aka datse hanyoyin sadarwa domin magance ayyukan yan bindiga

Katsina - Jaridar Channels tv ta ruwaito cewa tsagerun yan bindiga sun kai hari ƙauyen Barawa dake jihar Katsina, jihar da shugaba Buhari ya fito.

Rahotanni sun bayyana cewa yayin harin na ranar Lahadi, maharan sun kashe aƙalla mutun 4, tare da jikkata wasu da dama.

Wani mazaunin ƙauyen Barawa ya shaida wa manema labarai cewa yan tada ƙayar bayan sun farmaki kauyen ne a kan dandazon babura, kuma kowane ɗauke da makami.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Tsagerun yan bindiga sun harbe tsohon dan takarar gwamna a hanyar Abuja-Kaduna

Jihar Katsina
Da Duminsa: Miyagun yan bindiga sun kai sabon hari jihar Shugaba Buhari, sun kashe mutane da dama Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya kuma kara da cewa yan bindigan sun kwashe fiye da mintuna 90 suka aikata ta'asar su ba tare da samun turjiya daga jami'an tsrao ba, wanda yasa suka samu damar cin karen su babu babbaka.

Shin yan sanda sun san da faruwar lamarin?

Har zuwa yanzun da muke kawo muku wannan rahoton, rundunar yan sanda reshen jihar Katsina ba tace uffan ba game da faruwar harin kauyen Barawa.

Sai dai wata majiya mai ƙarfi ta tabbatar da cewa bayan yan bindigan sun fice, an tabbatar da mutuwar akalla mutum 4 a harin, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Kazalika har yanzun ba'a gano yawan adadin mutanen da yan bindigan suka ji wa raunuka kala daban-daban ba a yayin harin.

Haka nan kuma babu wani cikakken bayani kan cewa ko yan tada ƙayar bayan sun yi awon gaba da wasu mutane ko sun saci kayayyakin amfani na yau da kullum.

Kara karanta wannan

Zamu raya Sunnah ne, Mayakan Boko Haram sun yi awon gaba da yan mata 22

A wani labarin na daban kuma Mayakan Boko Haram sun sace yan mata 22 a jihar Neja, sun bayyana cewa auren su zasu yi

Wasu yan ta'adda da ake tsammanin mayakan Boko Haram ne sun sace yan mata 22 a wani kauyen jihar Neja.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun shaida wa mutanen kauyen cewa ba zasu cutar da su ba, aurensu za su yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel