Kada ka yarda matsin lamba ta sa ka saki Nnamdi Kanu, Kungiyoyin arewa ga Buhari

Kada ka yarda matsin lamba ta sa ka saki Nnamdi Kanu, Kungiyoyin arewa ga Buhari

  • Hadakar kungiyoyin arewa (CNG) ta soki bukatar shugabannin Ibo akan kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari na amincewa da sakin Nnamdi Kanu
  • Dama shugabannin Ibo sun kai ziyara fadar shugaban kasa a ranar Juma’a inda suka bukaci sakin Kanu amma Buhari ya kwatanta bukatar su da cewa tana da nauyi
  • Sai dai Kakakin CNG, Abdul-Azeez Suleiman a wata hira da ya yi da manema labarai ya ce shugabannin su na yunkurin dakatar da adalci ne kuma ta yuwu su ke daukar nauyin Kanu

Kano - Hadakar kungiyoyin arewa (CNG) ta nuna kin amincewarta da bukatar shugabannin Ibo akan kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari na sakin shugabannin masu rajin kafa kasar Biafara (IPOB).

Daily Trust ta bayyana yadda shugabannin Ibo suka kai wa Buhari ziyara a ranar Juma’a har fadarsa suna bukatar sakin Kanu inda shugaban kasar yace bukatar tana da nauyi.

Kara karanta wannan

An zabi Aisha Buhari a matsayin shugaba a kungiyar matan shugabannin kasashen Afrika

Kada ka yarda matsin lamba ta sa ka saki Nnamdi Kanu, Kungiyoyin arewa ga Buhari
Kungiyoyin arewa sun bukaci Shugaba Buhari kada ya saki Nnamdi Kanu. Hoto: The Cable
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma CNG ta kwatanta bukatar tasu a matsayin hanyar juyar da adalci, inda suka ce a bi da duk wadanda suka bukaci hakan a matsayin masu hada kai da taimaka wa Kanu wurin cutar da al’umma, Daily Trust ta ruwaito.

A wata tattaunawa da manema labarai su ka yi da kakakin kungiyar CNG, Abdul-Azeez Suleiman ranar Litinin, ya caccaki martanin da Buhari ya yi wa shugabannin Ibo.

Arewa zata ga laifin Buhari idan ya saki Kanu ta’addanci ya taso

A cewarsa:

“Arewa zata zargi Buhari da zama sila matsawar wata tarzoma ta tashi sakamakon sakin Kanu in har ya yarda shugabannin Ibo suka takura masa ya amince da bukatarsu.”

Suleiman ya ce hadakar kungiyoyin arewa tana nan tana bincike akan irin tarzoman da ta tashi a kudu maso yamma daga 2017 zuwa 2020 karkashin jagorancin IPOB wanda aka halaka fiye da ‘yan arewa 1,230 a bangarori daban-daban na yankin.

Kara karanta wannan

Labari da Hotuna: Yadda mata zasu iya taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya, Shugaba Buhari

Kadarori da kasuwancin ‘yan arewa na yankin sun halaka

Ya kara da cewa:

“Kasuwanci na miliyoyi, dukiyoyi da kadarori masu darajar gaske na ‘yan arewa dake zama a kudu maso yamma sun halaka bisa umarnin Nnamdi Kanu.”

Hadakar kungiyoyin ta kula da yadda bukatar da shugabanannin Ibo suka gabatar bisa takurawa yasa Buhari ta yi alkawarin duba a garesu tare da manta yawan sojoji, ‘yan sanda da sauran ‘yan Najeriyan da ‘yan IPOB suka halaka.

Ta kara da bayyana yadda malaman addinai na arewa suka dinga tausar ‘yan arewa akan kwantar da tarzoma da kuma hakuri a lokacin da kudu suka dinga kai wa mazauna can farmaki.

Duk mai son a saki Kanu makiyin Najeriya ne

Don haka ne Suleiman ya ce duk mai bukatar sakin Kanu yana da burin ganin ya tarwatsa Najeriya ne.

So yake yi ya mayar da ita filin daga wacce kowa zai baje kolin ta’addancinsa ya tsira ba tare da an hukunta shi ba.

Kara karanta wannan

Bukatar sakin Nnamdi Kanu babban lamari ne, amma zan yi shawara: Buhari ga Dattawan Igbo

CNG ta ja kunnen Buhari akan bin komai a tsari da kuma ba shari’a damar yin ayyukanta yadda ya dace.

Ya kara da cewa:

“Arewa ta daina zama tabarmar da ko wanne dan ta’adda zai kai wa farmaki sannan a zauna a zura ido ana kallo."

Tunda DSS ta kama Nnamdi Kano tsawon watanni, ba ta bar shi ya sauya tufafi ba, Lauyansa

A wani labarin, lauyan shugaban kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra ta IPOB, Ifeanyi Ejiofor, ya ce tunda jami’an tsaro na fararen kaya, DSS su ka kama Nnamdi Kanu, ba su bar shi ya sauya suttura ba.

A wata takarda wacce The Cable ta ruwaito lauyoyin Kanu, Ejiofor da Aloy Ejimakor sun sa hannu ranar Alhamis, sun bayyana cewa DSS ta na matukar cutar da Kanu.

Lauyoyin sun ce yanzu haka hukumar azabtar da duk mazaunin kurkukun da ya yi magana da Kanu tare da horar da shi saboda gaisuwa da ya yi da shugaban IPOB din, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tunda DSS ta kama Nnamdi Kano tsawon watanni, ba ta bar shi ya sauya tufafi ba, Lauyansa

Asali: Legit.ng

Online view pixel