Tunda DSS ta kama Nnamdi Kano tsawon watanni, ba ta bar shi ya sauya tufafi ba, Lauyansa

Tunda DSS ta kama Nnamdi Kano tsawon watanni, ba ta bar shi ya sauya tufafi ba, Lauyansa

  • Ifeanyi Ejiofor, lauyan shugaban kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu, ya ce tunda jami’an tsaro na fararen kaya, DSS su kama shi, sun hana shi sauya sutura
  • A wata takarda wacce Ejiofor da Aloy Ejimakor, lauyoyin Kanu su ka sanya hannu ranar Alhamis, sun bayyana irin cuturwar da ake masa
  • A cewar lauyoyin, abin ya tsananta don yanzu haka hukumar tana azabtar da masu gaisawa da Kanu a cikin gidan kurkuku a matsayin horarwa

Lauyan shugaban kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra ta IPOB, Ifeanyi Ejiofor, ya ce tunda jami’an tsaro na fararen kaya, DSS su ka kama Nnamdi Kanu, ba su bar shi ya sauya suttura ba.

A wata takarda wacce The Cable ta ruwaito lauyoyin Kanu, Ejiofor da Aloy Ejimakor sun sa hannu ranar Alhamis, sun bayyana cewa DSS ta na matukar cutar da Kanu.

Kara karanta wannan

Mai gida ya bar PDP da babatu, ya kori shugabanninta daga ofis a kan kudin haya

DSS ta hana Nnamdi Kanu sauya tufafi tun bayan kama shi watanni 4 da suka shude, Lauyansa
Nnamdi Kanu da lauyoyin da ke kare shi. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Lauyoyin sun ce yanzu haka hukumar azabtar da duk mazaunin kurkukun da ya yi magana da Kanu tare da horar da shi saboda gaisuwa da ya yi da shugaban IPOB din, The Cable ta ruwaito.

Su na hana Kanu ganin rana na sa’o’i 23 a kullum

Kamar yadda takardar ta zo:

“An rufe shi a dan karamin dakin kurkuk wanda yake yin sa’o’i 23 ba tare da ya ga hasken rana ba kuma ba tare da ya yi magana da wani ba.
“Ya yarda da cewa ana yin hakan ne don a azabtar da shi kuma a janyo masa cutar damuwa da tashin hankali.
“A cikin sa’a daya da ake barin sa ya fito, duk wani mazaunin kurkukun da ya yi masa magana ya na fuskantar azabtarwa saboda gaisuwa da shi balle kuma su yi wasu maganganu.

Kara karanta wannan

NCC ta ankarar da jama’a, ‘yan damfaran Iran su na harin na'urori da wayoyi 'Yan Najeriya

“Tun da gwamnati ta kama shi, ba ta taba ba shi damar sauya suttura ba ko kuma ya yi ibada ga mahaliccinsa. Sannan hukumar ta ki amincewa da kayan bautar da lauyoyinsa su ka kai masa.”

Sun kara da bayyana yadda DSS ta ki biyansa gilashinsa na ciwon idanu wadanda jami’an hukumar suka lalata yayin kici-kicin dauko shi daga Kenya.

Lauyoyin sun koka akan rashin ba shi damar ganawa da likitoci don duba lafiyarsa

Sun ce wannan ne ya yi sanadin cutar da idanunsa kwarai. An hana shi damar tattaunawa da lauyoyinsa.

A cewar lauyoyin, an hana shi barci da matashi wanda hakan ya janyo masa ciwon kirji, baya da makogwaro.

Lauyoyin sun koka akan yadda hukumar DSS ta hana shi ganin likita domin duba lafiyarsa sakamakon allurar da aka yi masa wacce ta yi sanadin baccinsa har aka maido da shi Najeriya.

Sun ce wannan ya janyo masa wahala wurin numfashi, bugun zuciya da kyar, ciwon gabobi da sauran su.

Kara karanta wannan

Manyan Lauyoyi sun ba Gwamnati shawarar yadda za a zauna lafiya da Kanu da Igboho

Kafa Ƙasar Biafra Da Oduduwa: Tsohon Mai Neman Takarar Shugaban Ƙasa Daga Arewa Ya Goyi Bayan Kanu da Igboho

A wani labarin, tsohon mai neman tikitin takarar shugabancin kasa, Adamu Garba, ya ce wadanda ke neman ballewa daga Nigeria su kafa kasashen Biafra da Oduduwa suna da ikon yin hakan, Daily Trust ta ruwaito.

Da ake hira da shi a daren ranar Laraba a shirin Daily Politics na Trust TV, ya ce ba laifi bane a kirkiri wata kasar daga Nigeria, amma akwai bukatar dogaro da kundin tsarin mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel