Zamfara: Ƴan bindiga sun yi wa dagaci yankan rago a gaban jama'a, kun kashe wasu 8

Zamfara: Ƴan bindiga sun yi wa dagaci yankan rago a gaban jama'a, kun kashe wasu 8

  • Wasu yan bindiga sun kutsa kauyen Tungar Ruwa a jihar Sokoto sun yi wa dagacin garin yankan rago
  • Mai magana da yawun yan sandan jihar Mohammed Shehu ya tabbatar da harin amma bai yi cikaken bayani ba
  • Wani mazaunin garin shima ya tabbatar da lamarin yana mai cewa 'yan bindigan sun halaka dagacin ne don yana basu matsala

Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun yi wa dagacin ƙauye yankan rago sun kuma kashe wasu mutane takwas a Tungar Ruwa a ƙaramar hukumar Anka na jihar Zamfara.

Lamarin ya faru ne a tsakar daren ranar Laraba kamar yadda Premium Times ta ruwaito. Ƴan bindigan sun shafe awanni yayin harin.

Zamfara: Ƴan bindiga sun yi wa dagaci yankan rago a gaban jama'a, kun kashe wasu 8
'Yan bindiga sun yi wa dagaci yankan rago a gaban jama'a, kun kashe wasu 8 a Zamfara. Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Mai magana da yawun yan sandan jihar Mohammed Shehu ya tabbatar da harin amma bai bada cikakken bayani ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Miyagun yan bindiga sun kai wani mummunan hari Kaduna, sun kashe mutane

Ƙaramar hukumar Anka na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin Zamfara da ke fuskantar hare-haren ƴan bindiga.

Wani majiya daga kauyen ya magantu kan yadda abin ya faru

Mutanen ƙauyen da suka bar gidajensu saboda hare-haren sun yi hijira zuwa hedkwatar hukumar da kuma kananan hukumomin Maru da Talata Mafara.

Wani majiya, Anas Mustapha ya shaidawa Premium Times cewa maharan sun shiga garin a kan babura suka fara hare-harbe a iska a yayin da suka nufi gidan dagacin ƙauyen.

Bayan isarsu gidan, sun fito da shi sannan suka yanka shi a gaban wasu mutanen sa da suka tara a wurin.

Mr Mustapha ya ce

"An kuma tabbatar wasu mutane takwas sun mutu bayan harin. Amma abin da muka fahimta shine dagacin ƙauyen yan bindigan suka zo kashewa. Ka san idan suka lura cewa wani shugaban mutane na basu matsala, kashe shi kawai suke yi nan take."

Kara karanta wannan

Mutum 2 sun mutu yayin da wasu yan bindiga suka yi yunkurin sace dan majalisa a wurin daura Aure

Ya kuma ce yan bindigan sun sace kayan abinci da dabobi a kauyen amma ba su kashe kowa ba.

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan bindigan sun yi wa yan sanda kwanton ɓauna sun kashe bakwai.

Sokoto: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da matar malamin addini, sun bakaci Naira miliyan 30 kudin fansa

A wani labarin, kun ji cewa 'yan fashin daji sun yi garkuwa da matar sakataren cocin Evangelical ta Afirka ta yamma, ECWA, reshen jihar Sokoto, Rabaran Oro Yakubu.

Jaridar SaharaReporters ta ruwaito cewa masu garkuwan sun bukaci a biya su Naira miliyan 30 kudin fansa kafin su sako ta.

An rahoto cewa an sace ta ne a hanyar Lambar Bakura zuwa Lambar Tureta yayin zuwa Sokoto daga Tsafe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel