Matasan ‘yan Najeriya 4 da suka ginawa iyayensu mata gida, daya daga cikinsu bata kai shekara 15 ba

Matasan ‘yan Najeriya 4 da suka ginawa iyayensu mata gida, daya daga cikinsu bata kai shekara 15 ba

Addu’ar kowasu iyaye shine ganin yaransu sun yi nasara a rayuwa domin su samu damar dogara da su a lokacin da tsufa ya zo masu.

Haka kuma burin ‘ya’ya shine son ganin sun kyautata wa iyayensu ta hanyar dauke duk wasu dawainiya nasu da zaran sun kawo karfi.

A yan baya-bayan nan, matasa kan nuna godiya ga iyayensu ta hanyar rage masu nauyi da kuma mallaka masu gidajen da suke mafarkin samu.

A wannan zaure, Legit.ng za ta jero maku wasu matasan yan Najeriya hudu da suka ginawa iyayensu mata gida.

1. Maazi Ogbannaya Okoro

Tun bayan da iska ya daga rufin kwanon tsohon gidansu, sai Okoro ya sha alwashin cewa idan har ya samu kudi masu yawa, zai yi wa mahaifiyarsa kyautar sabon gida.

Matasan ‘yan Najeriya 4 da suka ginawa iyayensu mata gida, daya daga cikinsu bata kai shekara 15 ba
Matasan ‘yan Najeriya 4 da suka ginawa iyayensu mata gida, daya daga cikinsu bata kai shekara 15 ba
Asali: Original

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda iyayen matashi suka nuna farin ciki mara misali yayin da ya duba sakamakon jarrabawar zama lauya

Bayan wasu shekaru masu yawa da shan wannan alwashi, dan Najeriyan ya cika shi. Okoro ya gina wa mahaifiyarsa gida mai dakuna hudu wanda aka kawata shi.

2. Emmanuella

Emmanuella, matashiyar mai barkwanci ta ja hankalin mutane a shekarar bara lokacin da ta ginawa mahaifiyarta gida na zamani.

Da take wallafa hoton ginin a Instagram, matashiyar yarinyar ta bayyana cewa ta gina gidan ne domin nuna godiya kan abubuwan da mahaifiyar tata tayi mata.

3. Somto

Mahaifiyar Somto ta dade tana korafi kan lamarin haya. Domin kawo karshen wannan lamari, sai matashin ya gina mata gida da taimakon kannensa.

Matasan ‘yan Najeriya 4 da suka ginawa iyayensu mata gida, daya daga cikinsu bata kai shekara 15 ba
Matasan ‘yan Najeriya 4 da suka ginawa iyayensu mata gida, daya daga cikinsu bata kai shekara 15 ba Hoto: @somtoSocial
Asali: Twitter

Da yake wallafa hoton a yanar gizo, an gano matashin tsaye kusa da mahaifiyarsa wacce ta cika da farin ciki a gaban gidan.

4. Mai wasan barkwanci Sir Balo

Mai wasan barkwancin ya kasance dan buga-buga domin ya taba sana’ar siyar da “gala” don daukar dawainiyar kansa.

Sir Balo wanda ya ginawa mahaifiyarsa gida mai dakuna takwas ya bayyana cewa ya kasance mai jiran shagon siyar da barasa a tsakanin 2014 da 2015.

Kara karanta wannan

Manyan gobe: Hazikan matasa 'yan Najeriya 3 da suka kera motocin a zo a gani da kansu

Manyan gobe: Hazikan matasa 'yan Najeriya 3 da suka kera motocin a zo a gani da kansu

A gefe guda, wasu matasan 'yan Najeriya sun nuna wa duniya cewa ana iya damawa da su a kowani yanayi, kuma a shirye suke su shiga a fafata da su a duniyar kera motoci.

Duk da tarin kalubale da suka fuskanta ta fuskacin kudi, kayan aiki da tallafi daga hukumomi, matasan sun kera motocin da ya ja hankalin mutane da yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel