Da Duminsa: Atiku ya tura wa Davido sako bayan mika kudin da aka tara masa ga marayu

Da Duminsa: Atiku ya tura wa Davido sako bayan mika kudin da aka tara masa ga marayu

  • Atiku Abubakar ya mika sakon jinjina da taya murnar zagayowar ranar haihuwa ga mawakin nan Davido
  • A yau ne aka yi shagalin zagayowar ranar haihuwar mayaki Davido, wanda a makon nan ya yi wani babban al'amari
  • Atiku ya yi masa addu'o'in karin shekaru da daukaka da kuma taya shi murna tare da iyalai da danginsa

Tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2019, Atiku Abubakar ya bayyana yabonsa ga mawaki David Adeleke (Davido) bisa tallafin da ya mika ga marayu a fadin Najeriya.

A makon da ya gabata ne Davido ya bayyana bukata ga abokai da masoyansa cewa, yana bukatar su tura masa kudade cikin asusun bankinsa domin shagalin murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Da Duminsa: Atiku ya tura wa Davido sako bayan mika kudin da aka tara masa ga marayu
Atiku Abubakar da Davido | Hoto: newsdiplomatng.com
Asali: UGC

Jim kadan bayan da ya tara sama N200,000, Davido ya bayyana cewa, zai mika kudin ne ga cibiyoyin marayu a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

An kama mai faskare saboda fizgar mazakutar mai gidansa da rashin jituwa ya shiga tsakaninsu

Da yake yaba masa, Atiku ya ce Davido yayi kokari da dabarar tallafawa na kasa da kirkiro har aka tara masa makudan kudade.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika, Atiku ya taya Davido murnar zagayowar ranar haihuwarsa tare da yi masa addu'o'i.

Atiku ya bayyana haken ne a rubutun da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Lahadi 21 ga watan Nuwamba.

A cewar Atiku:

"Ina tare da 'yan uwa da abokan arziki da miliyoyin masoyan ka wajen taya ka murnar zagayowar ranar haihuwa. Ina yi maka fatan karin shekaru cikin koshin lafiya, karin wakoki da ke samun lambar yabo da, da uwa uba, daga wasu."

Mawaki Davido ya bayar da kyautar miliyan N250 ga marayu a fadin kasar

A baya kunji cewa, shahararren mawakin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido ya bayar da kyautar kudi naira miliyan 250 ga marayu a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga da Sojojin sun yi musayar wuta a Imo kan umarnin zama a gida na IPOB

Mawakin wanda ya samu kyautar naira miliyan 200 daga abokan arziki cikin kwanaki biyu, ya sanar da bayar da kyautar kudin ga marayu a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, 20 ga watan Nuwamba.

Obi Cubana, Oba Elegushi, Otedola, E-Money na daga cikin wadanda suka tarawa Davido kudaden cikin awanni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel