Da dumi-dumi: Mawaki Davido ya bayar da kyautar miliyan N250 ga marayu a fadin kasar

Da dumi-dumi: Mawaki Davido ya bayar da kyautar miliyan N250 ga marayu a fadin kasar

  • Shararren mawakin kasar Davido ya bayar da kyautar kudi naira miliyan 250 ga marayu a fadin kasar
  • A yan kwanakin da suka gabata ne abokan arziki da na sana'a suka tarawa mawakin kudi kimanin naira miliyan 200 a matsayin kyauta don zagayowar ranar haihuwarsa
  • Sai dai a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 20 ga watan Nuwamba, mawakin ya ce ya bayar da kyautar kudaden ga marayu a kasar bayan ya kara shi ya zama N250m

Shahararren mawakin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido ya bayar da kyautar kudi naira miliyan 250 ga marayu a fadin kasar.

Mawakin wanda ya samu kyautar naira miliyan 200 daga abokan arziki cikin kwanaki biyu, ya sanar da bayar da kyautar kudin ga marayu a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, 20 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Gwamna Umahi ya magantu a kan fastocin yaken neman zabensa da suka bayyana

Da dumi-dumi: Mawaki Davido ya bayar da kyautar miliyan N250 ga marayu a fadin kasar
Da dumi-dumi: Mawaki Davido ya bayar da kyautar miliyan N250 ga marayu a fadin kasar Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Obi Cubana, Oba Elegushi, Otedola, E-Money na daga cikin wadanda suka tarawa Davido kudaden cikin awanni.

Davido ya bayyana a shafinsa na Instagram cewa zai bayar da dukka kudaden da aka tara mai bayan ya kara N50,000,000 ga marayu.

Ya kafa kwamitin rabon kudaden wadanda suka hada da farfesoshi uku da fasto daya.

Mawakin ya ce manufarsa shine ya mayar da tallafin wani al'ada na duk shekara domin bikin zagayowar ranar haihuwarsa.

Ya yi kira ga masoyansa da abokai a kan su ci gaba da mara masa baya kan wannan kudiri.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

“Ina mika godiyana ga abokaina, abokan aiki, masoya da jama’a a kan wannan karamci na soyayyarsa da suka nuna mun a yan kwanakin nan. A cikin wasana kamar kullun, na abokaina da abokan aiki da su tura mun kudi don bikin zagayowar ranar haihuwana.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: FG ta gargadi kungiyoyin kwadago ma'aikata kan amfani da kungiya ana karya doka

“Martani da sakamakon wasan ya wuce tunanina, yayin da na samu kimanin naira miliyan 200 cikin kasa da kwanaki biyu. Ina godiya sosai ya dukkannin wadanda suka bayar da kyautar guminsu kuma Ina godiya da karamcin.”

Kudi na magana: Masoya sun tarawa Davido sama da Naira miliyan 120 a ‘yan awanni

A baya mun kawo cewa shahararren mawakin Najeriya, David Adeleke wanda aka fi sani da Davido ya samu miliyoyin kudi daga jama’a bayan da ya nemi a tara masa kudi.

A lokacin da Legit.ng Hausa ta ke tattara wannan rahoto a ranar Laraba, 17 ga watan Nuwamba, 2021, sama da Naira miliyan 120 ne suka shiga asusun Davido.

Hakan na zuwa ne bayan mawakin ya yi magana a shafinsa na Instagram, inda yake tsokanar masoyansa da cewa su taimakawa sana’arsa da Naira miliyan daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel