An kama mai faskare saboda fizgar mazakutar mai gidansa da rashin jituwa ya shiga tsakaninsu

An kama mai faskare saboda fizgar mazakutar mai gidansa da rashin jituwa ya shiga tsakaninsu

  • Jami’an tsaron Amotekun na jihar Ogun da ke aiki da karamar hukumar Ijebu ta arewa sun kama wani mai sarar itace mai shekaru 40, Ogidan Yusuf
  • Ana zargin sa da laifin yankar mazakutar Ubangidansa, Oluwa Shakiru sannan ya ci zarafin matarsa duk saboda ya nemi amsar injin yanka katakonsa da ke wurinsa
  • Kwamandan Amotekun, David Akinremi ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Talata inda ya ce watanni biyu kenan da wanda ake zargin ya ke ta wasan buya da wanda ya yiwa aika-aikar

Ogun - Jami’an tsaron Amotekun na jihar wadanda ke aiki karkashin karamar hukumar Ijebu ta arewa sun kama wani mai sarar itace mai shekaru 40, Ogidan Yusuf.

Ana zarginsa da fizgar mazakutar Ubangidansa, Oluwa Shakiru sannan da cin zarafin matarsa saboda batan injin sarar katako, The Punch ta ruwaito.

An kama mai faskare saboda fizgar mazakutar mai gidansa da rashin jituwa ya shiga tsakaninsu
Jami'an Amotekun sun kama wani mai faskare da ya damki mazakutar mai gidansa. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Wanda ake zargin ya na yi wa wanda ya yiwa aika-aikar aiki ne a matsayin mai yankan katako kafin a kama shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwamandan rundunar Amotekun, David Akinremi ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.

A cewar Akinremi, lamarin ya faru ne bayan watanni biyu da mutumin ya ke ta wasan buya da ubangidansa akan ya batar masa da wani injin.

Ya kasa maido da injin din da aka ba shi ya yi aiki da shi

A cewar Kwamandan:

“Wanda ake zargin ya ki mayar da wani injin yankar katako da aka ba shi don ya yi aiki da shi inda yace masu gadin daji sun kwace a makwannin da su ka gabata.
“Yayin kokarin amso abin yankar katakon, tare da yunkurin rama cin zarafin da wanda ake zargin ya yiwa matarsa sai su ka fara dambe. Ana tsaka da hakan ya fizgi mazakutar ubangidan nasa wanda ya kusa cirewa daga nan ya tsere. Sai daga baya jami’anmu su ka jamo shi.

“An yi gaggawar wucewa da shi asibitin koyarwa na Olabisi Onabanjo inda ake kulawa da lafiyarsa. Shi kuma wanda ake zargin bayan ya amsa laifinsa an mika shi ga jami’an hukumar ‘yan sanda.”

'Yan sanda sun yi ram da wasu samari 2 bayan sun datse wa juna hannaye yayin kwasar dambe

A wani labarin, 'yan sanda sun yi ram da samari 2 bisa kama su dumu-dumu da laifin sare wa juna hannaye, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

An ruwaito yadda ‘yan sandan su ka kama Adamu Mohammed da Bukar Audu, bayan sun datse wa juna hannaye yayin wani fada da su ka tafka a Garin Alkali, karamar hukumar Dapchi da ke jihar Yobe.

Premium Times ta bayyana yadda Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, a ranar Litinin a Damaturu ya bayyana a wata takarda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel