Mu leka madafa: Dalla-dalla yadda ake hada wani nau'in Kuli-Kuli mai ban sha'awa

Mu leka madafa: Dalla-dalla yadda ake hada wani nau'in Kuli-Kuli mai ban sha'awa

Abinci na da matukar muhimmanci a kowace al'ada a duniya. Ba a bar Hausa da jama'ar Arewa a baya ba. 'Yan Arewa na da irin-iren abinci daban-daban wadanda duniya ta shaida ingancinsu kuma ake amfani dasu, daga ciki akwai kuli-kuli.

Kuli Kuli abinci mai karmamas hade da dandano mai dadi wanda ake yi da busasshiya kuma soyayyiyar gyada shahararren nauyin abinci ne a duniyar Arewacin Najeriya.

Kuli Kuli abinci ne mai sauki wanda za'a iya ci a kowane lokaci kuma an fi cinsa tare da garin rogo jikakke, kunu ko dai wani nau'in abincin kamar kwado da godoso idan an daka shi.

A yau dai Legit.ng Hausa ta tattaro muku yadda ake hada wani nau'in kuli-kuli cikin sauki daga gyada wanda zai ba ku sha'awa, kamar yadda Pulse ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikici kan leda ya sa matar aure ta cizge wa maƙwabciyar ta kunne da haƙoranta

Mu leka madafa: Dalla-dalla yadda ake hada wani nau'in Kuli-Kuli mai ban sha'awa
Kuli-Kuli dan Najeriya | Hoto: pulse.ng
Asali: UGC

Sinadaran hadin kuli kuli

 1. Kofuna 2 na gyada mara bawo, a tabbata an soya ta an barbada gishiri
 2. Man gyada
 3. Cokali 1 na dakakken barkono
 4. Cokali 1 da rabi na garin citta don karin dandano da kamshi
 5. Yankakken albasa (ba dole ba)

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda ake hadawa

 1. A nika gyada hade da citta har sai sun yi laushi. Hakanan ana iya amfani da injin sarrafa abinci mai karfi. Kar a bari ya niku ya hade sosai.
 2. A samu gyallen tata mai tsafta, a kwaba nikakkiyar gyadan a cikin tukunya sai a yi ta matse mai gwargwadon iyawa har sai ya zama tunkuza. Yawan man da aka iya matsewa cikin tunkuzar, yanayin karfin da kuli kulin zai yi.
 3. A zuba tunkuzar a cikin kwano sannan a zuba barkono dakakke, sai ya jujjuya shi da hannu.
 4. Daga nan sai a cura shi cikin siffar kananan kwallaye ko dogo kamar sanda. Ana iya cura shi ta siffofi masu yawa kamar mara shi da dai sauransu.
 5. Daga nan sai a soya man a cikin kasko har sai ya fara konewa. Za a iya jefa yankakken albashi don karawa man kamshi.
 6. Daga nan sai kuma a jefa curarren tunkusan cikin man gyadan mai zafi.
 7. A cire daga man ta hanyar amfani da matsami, idan ya tsame shikenan an gama kuli-kuli. Za a iya cinsa da garin rogo ko a kwado da dai sauran nau'ikan abinci.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Gwamna Umahi ya magantu a kan fastocin yaken neman zabensa da suka bayyana

Tsadar abinci: Gwamnatin Nijar za ta fara sayar da kayan abinci da kanta ga talakawa

A wani labarin, yayin da tsadar kayayyakin abinci ya addabi jamhuriyar Nijar, gwamnati ta yanke shawarar karbe ragamar sayar da abinci domin fara sayarwa da kanta.

A cewar rahoto, duk da cewa hakan zai taimaka wajen sayar da shi a farashi mai rahusa ga talakawan kasar, kasancewar 'yan kasar na fafutuka wajen samun wadataccen abinci a 'yan shekarun nan, lamarin ya jawo cece-kuce.

An samu martani daga bangarori daban-daban, kamar yadda aka ruwaito cewa, wasu da dama sun soki yunkurin, yayin da dama suke Allah-saka da ci gaban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel