Tsadar abinci: Gwamnatin Nijar za ta fara sayar da kayan abinci da kanta ga talakawa

Tsadar abinci: Gwamnatin Nijar za ta fara sayar da kayan abinci da kanta ga talakawa

  • Duba da yadda talakawa ke shan wahala, gwamnatin jamhuriyar Nijar ta yanke shawarar fara sayar da abinci da kanta
  • A rahoton da muka samu, gwamnati ta ce ta karbe ragamar sayar da kayan abinci da wasu daidaiku ke dashi a kasar
  • Lamarin ya jawo cece-kuce, inda wasu ke yabon yunkurin wasu daga cikin talakawa ke ganin hakan bai dace ba

Damagaram, Nijar - Yayin da tsadar kayayyakin abinci ya addabi jamhuriyar Nijar, gwamnati ta yanke shawarar karbe ragamar sayar da abinci domin fara sayarwa da kanta.

A cewar rahoto, duk da cewa hakan zai taimaka wajen sayar da shi a farashi mai rahusa ga talakawan kasar, kasancewar 'yan kasar na fafutuka wajen samun wadataccen abinci a 'yan shekarun nan, lamarin ya jawo cece-kuce.

Kara karanta wannan

Jami'ar Ilorin ta kori dalibin dan aji hudu da ya lakadawa lakcararsa dukan kawo wuka

Tsadar rayuwa: Gwamnatin Nijar za ta fara sayar da kayan abinci da kanta ga talakawa
Shugaban jamhuriyar Nijar, Bazoum Mohammed | Hoto: Niger Presidency
Asali: UGC

An samu martani daga bangarori daban-daban, kamar yadda aka ruwaito cewa, wasu da dama sun soki yunkurin, yayin da dama suke Allah-saka da ci gaban.

A wani sakon sautin da Legit.ng Hausa ta samo daga RFI, ta ce ministan cikin gida na jamhuriyar ta Nijar ne ya karbe ragamar sayar da abinci daga magadan gari domin ragewa talakawa radadi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tuni an tura wasiku ga wadanda ke da hannu a harkokin sayar da abinci a kasar domin sanar dasu wannan ci gaba, wanda ya fara a jihar Damagaram.

Abdu Sallau Kogo mukaddasin magatarka na ofishin gwamnan jihar Damagaram ya shaidawa wakilin RFI cewa:

"To idan ka dauki wannan misali, wasu jihohin ma hakanan ne, duk da dai wanda gaskiya abun basu ci kudi ba kamar jihar Damagaram.
"Saboda haka ne ministan cikin gida ya dauki kudurin cewa yanzu, an fidda sayar da abinci daga hannun marori mai da ta ga hannun gwamnati."

Kara karanta wannan

Abubuwa 17 da ya kamata ku sani a rahoton da kwamitin Endsars ya gabatar

Wannan ya faru ne sakamakon samun yawaitar sama da fadi da kudaden sayar da abinci ga talakawa a farashi mai rahusa daga magadan gari.

A halin yanzu, yawaitar sace kudin ya lalata abubuwa da dama da suka shafi sayar da abinci a farashi mai rahusa, wanda ya kai ga mika masu hannu a lamarin zuwa magarkama.

Wasu daga cikin magadan garin, sun bayyana gayon bayansu da yabo ga lamarin, inda suka bayyana cewa, hakan rage nauyi ne akansu.

Sai dai, a bangaren talakawan gari, wasu sun bayyana rashin jin dadinsu da wannan mataki, inda suka ce ba sa samun abin da suke so a hannun sabbin wakilan kamar yadda suke samu a hannun magadan gari.

Baya ga Nijar, Najeriya ma na fuskantar tsadar rayuwa, musamman wajen hauhawar farashin kayan abinci.

'Yan Najeriya sun sha yin korafi kan yadda gwamnati ta yi shuru ta bar 'yan kasuwa ke cin karensu ba babbaka wajen kara farashin kaya.

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: FG ta na kokarin karairaya farashin kayan abinci, Ministan noma

Maimakon duba farashin abinci, gwamnatin Najeriya ta bayyana bukatar dawo da haraji kan ababen sha a kasar, wanda zai kara farashin ruwan sha da sauran kayan shaye-shaye a kasar, kamar yadda kungiyar WAPAN ta yi ishara.

Sayen kayan abinci a Kogi da Jigawa ya fi Legas tsada yayin da farashi ya karu a Oktoba

A Najeriya kuwa, Hukumar Kididdiga ta kasa ta bayyana cewa farashin kayayyakin abinci a kasar ya sake tashi a watan Oktoban shekarar 2021, duk da faduwar farashin kayayyaki karo na 7 a jere zuwa kashi 15.99%.

NBS ta bayyana hakan ne a cikin sabon rahotonta na farashin kayan masarufi da ta buga a shafinta na yanar gizo a ranar Litinin, 15 ga Nuwamba, 2021.

A hakikanin gaskiya, adadin hauhawar farashin kayayyaki a Oktoba na 15.99% shine adadi mafi kankanta a cikin watanni 10 da suka gabata. Tun daga farkon shekarar 2021 (Janairu zuwa Oktoba), alkaluman hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya kai kashi 17.28%.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Gwamnatin Buhari za ta yi aikin canza taswirar Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel