Rikici kan leda ya sa matar aure ta cizge wa maƙwabciyar ta kunne da haƙoranta

Rikici kan leda ya sa matar aure ta cizge wa maƙwabciyar ta kunne da haƙoranta

  • Wani rikici ya hautsine tsakanin wata mata mai yara 4, Nwunye Ofo da makwabciyarta a ranar Laraba a karamar hukumar Enugu ta kudu da ke jihar Enugu
  • An samu bayanai akan yadda Ofo ta cizge wa Ogechi kunne cikin fushi saboda Ogechi ta bukaci sanin dalilin da ya sa Ofo ta ajiye mata leda a bakin kofa sannan suka sha cacar baki
  • Radadin azaba ya sa Ogechi ta ce ba za a barta a baya ba, inda ta gannara wa Ofo cizo a hannunta, dama kuma ba wani ga maciji su ke yi da juna ba

Jihar Enugu - A daidai titin Agulese Ugwueme a Akwuke da ke karamar hukumar Enugu ta kudu a jihar Enugu, wani rikici mai ban tsoro ya hutsine tsakanin mata biyu, The Punch ta ruwaito.

Read also

Yajin aiki: FG ta gargadi kungiyoyin kwadago ma'aikata kan amfani da kungiya ana karya doka

Nwunye Ofo, wata mata mai yara hudu ta cizge wa makwabciyarta, Ogechi kunne daya yayin da su ke tsaka da kwasar dambe.

Rikici kan leda ya sa matar aure ta cizge wa maƙwabciyar ta kunne da haƙoranta
Kwamishinan 'yan sandan jihar Enugu, CP Lawal Abubakar. Hoto: The Punch
Source: Facebook

The Punch ta tattaro bayanai akan yadda wacce aka yi wa aika-aikar, Ogechi, ‘yar asalin Ezza da ke jihar Ebonyi ta bukaci sanin dalilin da Ofo ta ajiye mata leda a bakin kofa.

Manema labarai sun fahimci yadda tambayar ta hassala Ofo wanda ya sa su ka hau cacar baki tsakaninsu wanda ya ja su ka fara ba hammata iska.

Wacce ake zargin ‘yar Ohafia ce da ke jihar Abia ta yi gaggawar dadumar kan Ogechi inda ta cizge mata kunne daya.

Ogechi mai yara 2 da ta ji azaba ta damki hannun Ofo ta gannara mata cizo.

Read also

Osinbajo masoyin musulmai ne, bai da boyayyar manufa - Kungiyar Kare Hakkin Musulmai

Dama makwabtan ba sa wani ga maciji

Makwabtansu yayin bayar da bayani akan lamarin sun bayyana yadda Ofo ta ke da sauran hassala.

Wakilin The Punch ya gano yadda makwabtan dama ba sa shiri saboda yaransu sun yi fada da juna.

Yawanci fadace-fadacen da ke tsakaninsu saboda shanya a igiya ne ko kuma a bakin rijiya wurin diban ruwa.

Wata mata da ke zama a gidan, Mama Uka ta ce dukansu su na da hayaniya.

A cewarta:

“Dama su na zaman doya da manja ne kuma wannan ba shi bane karo na farko da rikici ya taba hadasu sai dai ba su taba dambe ba sai jiya.”

‘Yan sanda sun bukaci su sasanta

An samu bayanai akan yadda su ka kai kara ofishin ‘yan sanda inda aka ba su shawarar sasantawa a gida sannan su koma su bayar da rahoto.

‘Yan sandan sun bukaci mijin wacce ta yi aika-aikar da ya biya duk wasu kudade da aka kashe a asibiti.

Read also

Borno: Arangama ta da 'yan ta'addan ISWAP a kan titi, Malamin makaranta

Jami’in hulda da jama’an rundunar, Daniel Ndukwe yace ba a sanar da shi komai ba dangane da lamarin.

Yadda direban mota ya cizge wa jami’in tsaro ɗan yatsa da haƙora sannan ya haɗiye yatsan

A baya, kun ji cewa wani direban motar haya da ba a gano ko wanene ba, a ranar Talata ya gannara wa wani jami'in tsaro na jihar Ebonyi cizo a yatsarsa ya kuma cizge yatsar, rahoton Premium Times ta ruwaito.

An samu bayanai akan yadda ya tsere da abin hawarsa bayan ya hadiye dan yatsan da ya cire.

An gano sunan jami’in tsaron Iboko Kenneth, wanda mummunan lamarin ya auku da shi kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Source: Legit.ng

Online view pixel