Nan da 2022 ku kara kudin lantarki da man fetur: Asusun Lamunin duniya ga Gwamnatin Najeriya

Nan da 2022 ku kara kudin lantarki da man fetur: Asusun Lamunin duniya ga Gwamnatin Najeriya

  • Asusun Lamunin duniya ta yi kira ga Gwamnatin Najeriya da cewa nan da Junairun sabon shekara a cire tallafin mai da lantarki
  • Idan Gwamnati ta cire wannan tallafi, kudin man fetur da na lantarki zai tashi kusan ninki biyu
  • Yan Najeriya sun tofa albarkatun bakinsu kan wannan shawara da IMF ta baiwa gwamnatin Najeriya

Asusun Lamunin duniya IMF a ranar Juma'a ya yi kira ga Gwamnatin Najeriya ta cire tallafin man fetur da na wutar Lantarki gaba daya a farko-farkon shekarar 2022.

Idan Gwamnati ta cire wannan tallafi, kudin man fetur da na lantarki zai tashi.

IMF ya bayyana hakan a jawabin da ta saki na ayyukan karshen 2021, inda ya ce cigaba da biyan kudin tallafi man fetur babban hadari ne rana goben tattalin arzikin Najeriya.

Kara karanta wannan

Jami'ar Soja ta gamu da cizon maciji cikin ban dakin gidanta dake barikin Soji, ta mutu

Jawabin yace:

"A yanzu dai, rashin tabbas da ake cikin na bukatar a cire tallafin man fetur da wutan lantarki, a sauya yadda akae karban haraji, sannan a inganta lamarin canji."
"Cire tallafin mai da lantarki gaba daya abune da ya kamata ayi da gaggawa, sannan kuma a taimakawa talakawa da wani abu na rage zafi."

IMF ya jaddada cewa lallai a cire wannan tallafi kamar yadda aka tanada a dokar kamfanin man fetur PIA 2021.

Asusun Lamunin duniya ga Gwamnatin Najeriya
Nan da 2022 ku kara kudin lantarki da man fetur: Asusun Lamunin duniya ga Gwamnatin Najeriya
Asali: Getty Images

A cire tallafin wutan lantarki

IMF ya cigaba da cewa cire tallafin wutan lantarki shime ayi da gaggawa nan zuwa Junairun 2022 kuma kada ayi jinkiri.

Yace:

"Akwia bukatar baiwa mutane taimako domin rage zafin wannan abu kan talakawa, musamman yanzu da abubuwa ke hauhawa."

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fara rabawa talakawa kudi N1.6bn a jihar Jigawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel