Jami'ar Soja ta gamu da cizon macijiya cikin ban dakin gidanta dake barikin Soji, ta mutu

Jami'ar Soja ta gamu da cizon macijiya cikin ban dakin gidanta dake barikin Soji, ta mutu

  • Macijiya ta yi sanadiyyar mutuwar wata hafsar Sojin saman Najeriya a birnin tarayya Abuja
  • Majiya ta bayyana cewa jinkirin da akayi a asibitin Soji NAF na cikin dalilan mutuwarta
  • Ita da kanta ta tafi asibitin NAF bayan cizon amma ba'a samu mai bada magani ba

Birnin Tarayya Abuja - Wata jami'ar hukumar mayakan saman Najeriya, Lance Kofur Bercy Ogah, ta gamu da ajalinta cikin ban daki yayinda macijiya ta cijeta a gidanta.

Jami'ar ta fuskanci cizon macijiyar ne yayinda take biyan bukatarta a bayin gida cikin barikin Sojin NAF Base dake Abuja.

Punch ta ruwaito cewa bayan cizon, Kofur Ogah ta kwashe yaran dake gidanta kuma ta kaisu wajen makwabta sannan ta garzaya asibitin Nigerian Air Force hospital amma lokaci ya yi.

Kara karanta wannan

Labari da duminsa: Tsohon sanatan APC ya yanki jiki ya fadi, ya rigamu gidan gaskiya

A rahoton, wannan abu ya auku ne da safiyar ranar Juma'a.

Wata majiya, a cewar Punch, ta bayyana cewa:

"Za ka tarar da muggan dabbobi irin wannan a barikin. Mazauna na gamuwa da macizai sosai."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"An sanya magunguna a gidajen kwanan nan amma an tsallake nata saboda ba ta nan lokacin. Da yiwuwan macijin ya boye a bayinta."
"Bayan cizon macijin ta kai yaronta da wata yar uwarta wajen makwabta sannan ta garzaya asibitin NAF."

Jami'ar Soja ta gamu da cizon maciji
Jami'ar Soja ta gamu da cizon macijiya cikin ban dakin gidanta dake barikin Soji, ta mutu Hoto: Punch
Asali: Facebook

Me ya faru da taje asibiti?

Majiya ta cigaba da cewa jami'ar ta mutu a asibitin ne saboda dalilai da dama wanda ya hada da rashin duba ta da wuri.

A cewar majiyar:

"Da ta isa asibiti, sai da aka dau lokaci kafin yi mata allurar maciji. Bayan rashin magani, na samu labarin cewa wanda ke da hakkin bada magunguna ba ya nan."

Kara karanta wannan

Daliba a jami'ar Umaru Yar’adua ta sha piya-piya don saurayinta ya rabu da ita, an kaita asibiti

"Hakazalika sashen jikin da macijin ya cijeta na cikin dalilan da yasa ta mutu."

Yunkurin ji daga bakin Kakakin hukumar NAF, Edward Gabkwet, ya ci tura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel