Osinbajo masoyin musulmai ne, bai da boyayyar manufa - Kungiyar Kare Hakkin Musulmai

Osinbajo masoyin musulmai ne, bai da boyayyar manufa - Kungiyar Kare Hakkin Musulmai

  • Kungiyar Kare Hakkin Musulmai (MURIC) ta magantu a kan zargin da ake yi wa mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo na kasancewa mai akidar addini
  • MURIC ta bayyana cewa sabanin zargin da ake masa, Osinbajo mutum ne mai kaunar Musulmai duk da kasancewarsa Kirista kuma babban fasto
  • Ta ce binciken da ta gudanar ya nuna cewa akwai Musulmai 18 da ke aiki a karkashin ofishinsa

Kungiyar Kare Hakkin Musulmai (MURIC) ta bayyana cewa mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo yana kaunar Musulmai duk da kasancewarsa Kirista kuma babban fasto.

Kungiyar na mayar da martani ne ga wani zargi da aka yi wa Osinbajo na cewa yana da wata manufa ta addini ta hanyar nada kiristoci da yawa a gwamnati, The Cable ta rahoto.

Osinbajo masoyin musulmai ne, bai da boyayyar manufa - Kungiyar Kare Hakkin Musulmai
Osinbajo masoyin musulmai ne, bai da boyayyar manufa - Kungiyar Kare Hakkin Musulmai Hoto: The Cable
Asali: UGC

A wata sanarwa da ta saki a ranar Laraba, 17 ga watan Nuwamba, ta hannun daraktanta, Ishaq Akintola, MURIC ta ce ta gudanar da wani bincike kan lamarin kuma ta gano cewa karya ne.

Kara karanta wannan

Rahoton EndSARS: HURIWA ta bukaci Buhari ya fatattaki Lai Mohammed kan karyar da ya zuga

MURIC ta ce mataimakin shugaban kasar na karbar Musulmai hannu bibbiyu kuma ya nada kimanin su 18 mukami a ofishinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyar ta ce akwai bukatar ta yi magana don kare Kiristoci nagari da suke yin abin da ya dace.

Jawabin kungiyar ya zo kamar haka:

"Shafa bakin fenti, bata suna, labaran karya da fadin abu ba yadda yake ba baya daga cikin halayen Musulmai. Bai taba zama daga cikinmu ba. Cutar da wanda bai ji ba bai gani ba bakon abu ne ga kwayar halittar mu. Maimakon su rataya ayyukansu a wuyan abokan adawarsu, Musulmai kan tsaya tsayin daka idan sune ke da laifi. Sun gwammace a hukunta su a nan duniya domin su kubuta daga azabar lahira.
"Wadandca suka zalunce mu ne ke kokarin ganin cewa su ne suka fara kuka a kodayaushe alhalin su ne azzalumai. Babu wata kungiya ta Musulunci ta gaskiya da za ta shiga barna, karya, yaudara da makirci. Kungiyoyin Musulunci na gaskiya a bayyane suke. Kuna iya karantar su kamar yadda kuke karanta littafi.

Kara karanta wannan

Lamari ya yi zafi, dattawan Arewa sun zauna don neman mafita ga matsalolin Arewa

“Wadannan halaye su ne ke damun mu tun lokacin da aka fara cece-kuce game da zargin da ake yi wa mataimakin shugaban kasa Osinbajo na manufar addini. Mujaddadi Uthman Bin Fudi ya ce ‘Zuciya kamar rauni ne, gaskiya ce kadai za ta iya warkar da ita. Lamarinmu ya yi sanyi kuma ta wurin gaya wa duniya abin da muka sani ne kawai za mu iya samun kwanciyar hankali.
“A yayin bincikenmu, mun ci karo da labarin da wata musulma mai taimakawa shugaban kasa a ofishin mataimakin shugaban kasa ta rubuta. Labarin wanda ya fito kwanan nan a shafukan sada zumunta, ya tabbatar da akwai ma'aikata Musulmai 18 a ofishin Osinbajo. Wajibi ne a kan wadanda suka zargi mataimakin shugaban kasar da kaida na Kiristanci da su tabbatar da cewa an saki duk sunayen musulmin da ke ofishin mataimakin shugaban kasa ne domin su gamsar da Musulman Najeriya cewa mataimakin shugaban kasar ba makiyin Musulmi ba ne kuma ba azzalumi ba ne.”

Kara karanta wannan

Gumi ya caccaki 'yan aware: Igboho da Kanu ne suka kunna wutar rikicin Fulani a kudu

Kungiyar ta ce ta kuma gano cewa wani Abdul Rahman Ipaye, Musulmi, shine babban jami'i a ofishin mataimakin shugaban kasar.

A ruwayar Daily Post, kungiyar ta ce koda dai ba za ta marawa wanda ba Musulmi baya ba wajen zama shugaban kasa a 2023, hakan ba zai hana ta fadin gaskiya ba, inda ta ce babu wata alaka tsakaninta da mataimakin shugaban kasar.

Daram-dam-dam: Osinbajo bai hakura da neman Shugaban kasa a 2023 ba inji Kungiya

A wani labari na daban, wata kungiya mai suna The Progressive Consolidation Group, tace tana kokarin ganin Yemi Osinbajo ya zama shugaban kasa a zaben 2023.

Wannan kungiya ta magoya bayan mataimakin shugaban kasar ta fito tana musanya batun cewa Osinbajo ya hakura da neman takarar shugaban kasa.

Punch ta rahoto PCG tana cewa aikin da ke gaban Farfesa Osinbajo a yanzu shi ne maida hankali kan nauyin da ke gabansa na mataimakin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Kungiyar PDP ta nemi Gwamna Wike ya nemi takarar kujerar shugaba Buhari a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel