Yadda direban mota ya cizge wa jami’in tsaro ɗan yatsa da haƙora sannan ya haɗiye yatsan

Yadda direban mota ya cizge wa jami’in tsaro ɗan yatsa da haƙora sannan ya haɗiye yatsan

  • A ranar Talata wani direban mota a jihar Ebonyi ya kama babban dan yatsan jami’in tsaro sannan ya gannara masa cizo
  • An samu bayanai akan yadda bayan cizge yatsan ya hadiye shi sannan ya yi gaggawar jan motarsa ya tsere cikin hanzari
  • Lamarin ya auku na a kan kwanar Onuebonyi da ke cikin Abakaliki yayin da jami’an tsaron ma’aikatar ci gaban babban birnin su ke kan aiki

Jihar Ebonyi - Wani direban motar haya da ba a gano ko wanene ba, a ranar Talata ya gannara wa wani jami'in tsaro na jihar Ebonyi cizo a yatsarsa ya kuma cizge yatsar, rahoton Premium Times ta ruwaito.

An samu bayanai akan yadda ya tsere da abin hawarsa bayan ya hadiye dan yatsan da ya cire.

Kara karanta wannan

Yajin aikin ASUU: FG za ta rabawa jami’o’i biliyan N22.72 a ranar Laraba – Ministan Buhari

Yadda direban mota ya cizge wa jami’in tsaro ɗan yatsa da haƙora sannan ya haɗiye yatsan
Direban mota ya cizge wa jami’in tsaro ɗan yatsa da haƙora sannan ya haɗiye yatsan. Hoto: The Nation
Asali: UGC

An gano sunan jami’in tsaron Iboko Kenneth, wanda mummunan lamarin ya auku da shi kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lamarin ya auku ne a kan kwanar Onuebonyi a cikin Abakaliki yayin da jami’an tsaron ma’aikatar ci gaban babban birnin jihar su ke kan aiki.

Ma’aikatan sun tsattsaya bakin hanya ne don tabbatar da mutane sun bi dokokin kan titi a cikin babban birnin jihar.

Hakan ya biyo bayan sauya tasha da masu ababen hawa su ka yi zuwa tashar da gwamnati ta gina musu, Akubaraoha Central Park.

Yayin da su ka isa kwanar Onuebonyi, sun ga direbobi su na lodin fasinjoji.

Wani jami’in tsaro, Kenneth ya yi yunkurin kama wani direba, amma sai direban ya yi kukan kura ya kama dan yatsansa da cije shi har sai da ya cizge.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan ISWAP sun kai hari sansanin soji a Borno, suna ta musayar wuta da sojoji

An samu bayanai akan yadda direban ya hadiye dan yatsan sannan ya tsere da abin hawansa.

Jami’in tsaron ya na asibiti

An yi gaggawar wucewa da Kenneth asibitin koyarwa na tarayya na Alex Ekwueme, Abakaliki.

Kwamishinan ci gaban babban birnin jihar, Onyeka Nwebonyi, ya kwatanta lamarin a matsayin mummunan al’amari.

A cewarsa:

“Mummunan lamari ne ace direba ya kai wa jami’in tsaro farmaki ta hanyar cizge mishi yatsa. Wannan lamari ya kazanta kuma kauyanci ne.
“Ina so in roki direbobi da su kiyaye mu, saboda jami’an tsaro su na da cikakken iko kuma muna bin dokoki cikin ayyukanmu ne.”

Nwebonyi ya ce za a ci gaba da bincike akan wannan lamarin kuma za a dauki mataki don gudun hakan ya maimaita kansa.

'Yan sanda sun yi ram da wasu samari 2 bayan sun datse wa juna hannaye yayin kwasar dambe

A wani labarin, 'yan sanda sun yi ram da samari 2 bisa kama su dumu-dumu da laifin sare wa juna hannaye, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya ta bayyana abin da ya sa mutane suke wahala, ba su samun abin yi

An ruwaito yadda ‘yan sandan su ka kama Adamu Mohammed da Bukar Audu, bayan sun datse wa juna hannaye yayin wani fada da su ka tafka a Garin Alkali, karamar hukumar Dapchi da ke jihar Yobe.

Premium Times ta bayyana yadda Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, a ranar Litinin a Damaturu ya bayyana a wata takarda.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel