Yajin aiki: FG ta gargadi kungiyoyin kwadago ma'aikata kan amfani da kungiya ana karya doka

Yajin aiki: FG ta gargadi kungiyoyin kwadago ma'aikata kan amfani da kungiya ana karya doka

  • Gwamnatin tarayya ta gargadi ma'aikata kan sabuwar al'adar kulle ofishoshi da suka dauka a kwanakin nan
  • Wannan na zuwa ne bayan da wata kungiyar ma'aikata ta yi amfani da dama wajen rufe ofishin matar Ngige
  • A cikin sanarwar da aka fitar, gwamnati ta yi gargadin cewa, hakan ya saba doka, kuma lallai za a iya daukar mataki

Gwamnatin tarayya ta ce za ta dauki cikakken matakin doka a kan wadanda ke ci gaba da tsallake layi a cikin rigar kungiyanci ta ma'aikata.

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Sen. Chris Ngige ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da Mista Charles Akpan, mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar ya fitar ranar Talata a Abuja, Vanguard ta ruwaito.

Yajin aiki: FG ta gargadi kwadago ma'aikata kan amfani kungiya ana karya doka
Chris Ngige, Ministan kwadago da samar da ayyuka | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Ma’aikatan ma’aikatar ciniki da zuba hannun jari sun rufe kofar shiga ma’aikatar a ranar Larabar da ta gabata a yayin wata zanga-zangar neman a tsige sakatariyar dindindin, Evelyn Ngige, wadda ita ce uwargidan ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige.

Kara karanta wannan

2022: Kano ta ware miliyan N800 domin magance talauci da rashin aiki a tsakanin mata

Daily Trust ta ruwaito cewa, an zargi Misis Ngige da rashin kula da jin dadin ma’aikatanta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai ministan, Ngige, ya bukaci shugabannin kungiyar da su wayar da kan mambobinsu a kan hakkinsu da matsayinsu tare da kiransu ga bin doka da oda.

Ya ce gwamnati ba za ta nade hannayenta ba yayin da abin da ya kamata ya zama cikin kwanciyar hankali na kungiyoyin "ya ketare iyakar doka".

Ya ce:

“Gwamnatin tarayya ta ga yadda aka kulle ofisoshin karamin ministan kasuwanci da sakatariyar dindindin na ma'aikatar kasuwanci da saka hannun jari na tsawon kwanaki ta hanyar tayar da hankali daga kungiyoyin ma'aikata, tare da hana sauran ma'aikata da jami'an gwamnati gudanar da ayyukansu.
“Hakazalika, cibiyar horar da ‘yan kasa da jagoranci tana kulle-kulle tun ranar Litinin, 15 ga Nuwamba, 2021, inda aka hana sabon Darakta Janar na hukumar, Adesoji Eniade, karbar mukaminsa.

Kara karanta wannan

Yajin aikin ASUU: FG za ta rabawa jami’o’i biliyan N22.72 a ranar Laraba – Ministan Buhari

“Muna kara gargadin cewa munanan dabi’un da ke faruwa a yayin yajin aiki da sunan kange ma’aikata na iya fuskantar sassan doka da suka dace na kundin laifuffuka da kuma hukunta su yadda ya kamata. Rashin sanin doka ba hujja ba ce."

Jami'ar Ilorin ta kori dalibin dan aji hudu da ya lakadawa lakcararsa dukan kawo wuka

A wani labarin, hukumar gudanarwar jami’ar Ilorin ta kori wani dalibi mai suna Salaudeen Waliu Aanuoluwa na tsangayar nazarin ilmin halittu, bayan da aka same shi da laifin cin zarafin wata malamar jami’ar, Misis Rahmat Zakariyau.

A baya mun kawo muku rahoton yadda dalibin jami'ar dan aji hudu ya lakadawa lakcararsa dukan kawo wuka a harabar jami'ar saboda kin taimakonsa.

Wata sanarwa da Daraktan hulda na Jami’ar, Mista Kunle Akogun, ya fitar, ta bayyana cewa kwamitin ladabtarwa na dalibai ne ya yanke hukuncin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel