Hotuna: Ganduje ya jagoranci manyan yan siyasa wajen tarbar Tinubu yayin da ya isa Kano don ta’aziyyar Dangote

Hotuna: Ganduje ya jagoranci manyan yan siyasa wajen tarbar Tinubu yayin da ya isa Kano don ta’aziyyar Dangote

  • Gwamna Abdullahi Ganduje ya jagoranci manyan yan siyasa a Kano wajen yi wa jagoran jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu maraba da zuwa
  • Tinubu ya ziyarci jihar Kano a ranar Juma'a, 19 ga watan Nuwamba, domin yin ta'aziyyar mutuwar kanin mai kudin Afrika, Sani Dangote
  • Jigon na APC da tawagarsa sun kuma ziyarci unguwar Koki domin yin ta'aziyya ga Alhaji Aminu Dantata

Jihar Kano - Jagoran jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Bola Tinubu, ya ziyarci jihar Kano a ranar Juma'a, 19 ga watan Nuwamba.

Tinubu ya ziyarci jihar Kano ne domin gaisuwar ta'aziyya ga mai kudin Afrika, Aliko Dangote, kan rashi da yayi na kaninsa.

Allah ya yiwa marigayin, Sani Dangote, wanda ya kasance mataimakin shugaban rukunin kamfanin Dangote rasuwa a ranar Lahadi, a kasar Amurka.

Kara karanta wannan

Ni da mahaifiyata muna kallo lokacin da aka zare ran kanina amma babu yadda muka iya - Dangote

Ganduje ya jagoranci manyan yan siyasa wajen tarbar Tinubu yayin da ya isa Kano don ta’aziyyar Dangote
Ganduje ya jagoranci manyan yan siyasa wajen tarbar Tinubu yayin da ya isa Kano don ta’aziyyar Dangote Hoto Independent
Asali: UGC

Tinubu ya samu tarba daga gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, mataimakinsa, Nasir Gawuna da sauran manyan yan siyasar jihar a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, jaridar Independent ta rahoto.

An tattaro cewa kai tsaye ayarin motocin Tinubu suka tafi unguwar Koki domin yin ta'aziyya ga Alhaji Aminu Dantata.

Hakazalika ya ziyarci mai kudin Afrika, Aliko Dangote a gidansa na Kano da ke unguwar Nasarawa GRA.

Ganduje ya jagoranci manyan yan siyasa wajen tarbar Tinubu yayin da ya isa Kano don ta’aziyyar Dangote
Ganduje ya jagoranci manyan yan siyasa wajen tarbar Tinubu yayin da ya isa Kano don ta’aziyyar Dangote Hoto: qed.ng
Asali: UGC

A sakon ta'aziyyarsa, Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin dan Lagas kuma babban dan Najeriya. Ya kuma bayyana cewa kudi baya siyan rai kuma babu abun da mutum zai iya yi idan lokaci yayi, rahoton Vanguard.

Ya yi kira ga iyalan marigayin da su dauki hakuri da ci gaba da yi masa addu'an samun dacewa.

Kara karanta wannan

Kungiyar 'Edo Volunteers for Tinubu 2023' tana goyon bayan ƙusan APC a zaben 2023

Tinubu ya ce:

"Ba wai mun zo nan don yi maka ta'aziyya ko rarrashinka bane kawai, mun zo nan ne domin muyi makokin dan uwanmu a tare.
"Sani ba naka bane kai kadai. Dan Lagas ne kuma babban dan Najeriya kuma aboki, dan uwanmu mu dukka.
"Ni ba mai wa'azi bane, amma na san ciwon rashin makusanci, musamman kani.
"Allah ya baka karfin jure wannan rashi. Rashin nan ya shafi dukkanmu.
"Allah ya baka tsawon rai, ya barka cikin koshin lafiya, ya bar ahlin cikin koshin lafiya, ya baka nutsuwar zuciya da ikon cin jarrabawar Allah madaukakin sarki.
"Ya kasance mai bayarwa kuma mai karba kuma zai iya yin komai a duk lokacin da ya so."

Ni da mahaifiyata muna kallo lokacin da aka zare ran kanina amma babu yadda muka iya - Dangote

A baya mun kawo cewa daga karshe mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote, ya magantu a kan rasuwar kaninsa, Alhaji Sani Dangote.

Kara karanta wannan

Hotunan Gwamna Zulum yaje ta'aziyyar Janar din Sojoji da ISWAP ta kashe, ya baiwa iyalansa Miliyan N20m

Da ya tarbi jagoran jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a gidansa da ke Kano, a ranar Juma'a, 19 ga watan Nuwamba, Dangote ya ce mahaifiyarsu da yaran Sani na a wajen da aka dauki ran marigayin.

Ya ce ya fi masu radadi a lokacin da likitoci suka fada masu cewa dan uwansa na da kimanin awa daya da yayi masa saura kafin ya mutu, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel