Kungiyar 'Edo Volunteers for Tinubu 2023' tana goyon bayan ƙusan APC a zaben 2023

Kungiyar 'Edo Volunteers for Tinubu 2023' tana goyon bayan ƙusan APC a zaben 2023

  • Kungiyar nan ta Edo Volunteers for Tinubu 2023 ta na tare da tsohon Gwamnan Legas a zabe mai zuwa
  • Shugabar Edo Volunteers for Tinubu 2023, ta bayyana dalilinsu na goyon bayan Asiwaju Bola Tinubu
  • Owolabi Adetutu tace darajar kasar nan za ta karu a ko ina idan aka ce yau Tinubu ne a kan mulkin

Edo - Wata kungiya da ke goyon-bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu mai suna Edo Volunteers for Tinubu 2023, ta fara yi masa yakin neman zama shugaban kasa.

Kungiyar Edo Volunteers for Tinubu 2023 ta tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa martaba da kimar kasar nan zai karu a Duniya idan Bola Tinubu ya samu mulki.

Shugabar wannan kungiya ta kasa, Misis Owolabi Adetutu, ta bayyana wannan a wani jawabi da ta fitar yayin da ake shirin bikin rantsar da kwamitin kungiyar.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Dalilin da yasa wajibi shugaba Buhari da Arewa su goyi bayan Bola Tinubu a 2023

Kamar yadda Vanguard ta rahoto, za a gudanar da taron kaddamar da ‘ya ‘yan kungiyar ne a garin Benin, jihar Edo a ranar Asabar, 20 ga watan Nuwamba, 2021.

Wadanda za su halarci bikin kaddamar da kwamitin kungiyar sun hada da wasu manyan ‘yan siyasar jihar Edo da na yankin kudu maso kudancin kasar nan.

Rahoton yace daga cikin wadanda za su halarci bikin rantsarwar akwai Hon. Razaq Bello-Osagie, da Dr. Bamidele Agbadua wanda zai gabatar da laccar musamman.

Bola Ahmed Tinubu
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: @JournalistKC
Asali: Facebook

Najeriya za ta samu cigaba ta fuskoki da dama idan ya zama shugaban kasa. - Adetutu

Jawabin na Owolabi Adetutu ya ce kungiyar ta na goyon bayan takarar Tinubu ne saboda ya nuna ya san yadda zai bunkasa tattalin arziki ya kuma samar da tsaro.

Kara karanta wannan

'Yan kasuwa a Legas sun yi zanga-zangar nuna adawa da 'yar shugaban APC Tinubu

“Yayin da Duniya ta karkato ga Afrika domin a kulla sababbin yarjejeniya, mu na da dama ta musamman da za mu kulla a lakocin da za su kawo cigaba da nasara ga matasa, manoma, mata, masu aikin hannu, da sauransu.”
“Asiwaju Tinubu mutum ne da ya san aiki. Ba bako ba ne a siyasar Duniya, kuma zai yi amfani da mutanensa wajen kare martaba da darajar Najeriya, har ayi nasarar jawowa kasar hannun jari.”

'Yan tawaren APC sun ce sai Tinubu

A baya an ji Wogu Boms yana cewa alamu sun nuna tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu ne zai karbi mulkin Najeriya a zaben shugaban kasar da za ayi a 2023.

Boms da wani takwarsa da yake goyon bayan Tinubu ya samu mulki, sun buki girji da cewa su ne su ka sa Buhari ya zama shugaban kasa, kuma za su sa Tinubu a kujerar.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya samu gagarumin goyon bayan sarakuna 300 domin ya gaji kujerar Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel