Gwamna Zulum yaje ta'aziyyar Janar din Sojoji da ISWAP ta kashe, ya baiwa iyalansa Miliyan N20m

Gwamna Zulum yaje ta'aziyyar Janar din Sojoji da ISWAP ta kashe, ya baiwa iyalansa Miliyan N20m

  • Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya kai ziyarar ta'aziya ga iyalan marigayi Janar Dzarma Zirkushu
  • Zulum ya baiwa iyalan tallafin kuɗi kimanin miliyan N20m kuma ya jajantawa mata da yayan marigayin
  • Yace mutanen jihar Borno ba zasu taba mancewa da sadaukarwan gwarazan sojojin ba

Kaduna - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya jagoranci tawaga zuwa ta'aziyyar marigayi Birgediya Janar Dzarma Zirkushu.

Gwamnan ya gana da iyalan marigayin a sansanin soji na Ribadu dake jihar Kaduna, kuma nan take ya bada umarnin sakin miliyan N20m ga iyalan don tallafa musu.

A wata sanarwa da ofishin gwamna Zulum ya fitar a dandanlin Facebook, Kakakin gwamnan, Malam Isa Gusau, yace nan take aka tura musu kudin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An yi jana'izar Sani Dangote a Kano

Gwamna Zulum
Gwamna Zulum yaje ta'aziyyar Janar din Sojoji da ISWAP ta kashe, ya baiwa iyalansa Miliyan N20m Hoto: The Governor Of Borno State
Asali: Facebook

Gusau ya ƙara da cewa gwamnatin jihar Borno zata tallafawa iyalan sojojin da aka kashe tare da marigayi janar Dzarma Zirkushu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Su waye a tawagar Zulum?

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwa, da kwamandan rundunar soji ta Division One, Birgediya Janar T. Opuene, sune suka tarbi Zulum a filin jirgi.

Zulum ya dira Kaduna ta'aziyya tare da sanatocin jihar Borno uku, Kashim Shettima, Mohammed Ali Ndume da Abubakar Kyari; mambobin majalisar dokoki biyu, Dr. Haruna Mshelia da Ahmad Jaha.

Zulum ya gana da iyalan marigayin

Gwamnan Zulum ya yiwa matar marigayin ta'aziyya, Blessing Zirkushu, da kuma ƴaƴanta guda 5, bayan ɗan uwan marigayin, Gurdebil Zirkushu, ya tarbe shi da sauran wasu iyalai.

Zulum ya jajantawa iyalan baki ɗaya, kuma ya roke su kada su bar kyakkyawar turbar da marigayi birgediya janar ɗin ya bar musu.

Kara karanta wannan

Yadda tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Kano ya canza gidan siyasa sau 6 a shekara 7

A jawabinsa yace:

"Mutanen Borno zasu cigaba da girmama janar ɗin sojoji da sauran jami'an sojin da suka mutu tare da shi."
"Kazalika ba za su mance da sauran sojojin da suka sadaukar da rayuwarsu da ma waɗan da ke fagen daga a yanzu."

Hotunan ta'aziyyar

Zulum
Gwamna Zulum yaje ta'aziyyar Janar din Sojoji da ISWAP ta kashe, ya baiwa iyalansa Miliyan N20m Hoto: The Governor Of Borno
Asali: Facebook

Matar marigayi
Gwamna Zulum yaje ta'aziyyar Janar din Sojoji da ISWAP ta kashe, ya baiwa iyalansa Miliyan N20m Hoto: The Governor of Borno
Asali: Facebook

Gwamna Zulum
Gwamna Zulum yaje ta'aziyyar Janar din Sojoji da ISWAP ta kashe, ya baiwa iyalansa Miliyan N20m Hoto: The Governor of Borno
Asali: Facebook

A wani labarin kuma Gini ya sake kifewa kan mutane a Jihar Legas, Jami'ai sun fara aikin ceto

Bayan kifewar gini mai hawa 21 a jihar Legas, a yau Laraba an sake samun wani gini da ya rushe kan jama'a a yankin Badagry.

Rahoto ya nuna cewa tuni jami'an kwana-kwana da masu ceto suka dira wurin, kuma an ceto wasu mutum 5 a raye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel