Gwamnan PDP ya bi sahun Sheikh Gumi, Ya Bayyana hanyar da Buhari zai bi ya kawo karshen yan bindiga

Gwamnan PDP ya bi sahun Sheikh Gumi, Ya Bayyana hanyar da Buhari zai bi ya kawo karshen yan bindiga

  • Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo, ya shawarci gwamnatin tarayya ta maida hankali kan ilimantar da yara tun daga matakin farko
  • A cewar gwamnan wannan hanya ce mafi sauki ta kawo karshen matsalar yan bindiga da Najeriya ke fama da ita
  • Ya kuma koka kan yadda yara da suka kammala karatun sakandire suka fi maida hankali wajen fita kasashen waje

Edo - Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya roki gwamnatin tarayya da jihohi su maida hankali kan ilimi a matakin farko a matsayin hanyar kawo karshen ayyukan yan bindiga a Najeriya.

Dailytrust ta rahoto cewa gwamnan ya nuna matukar damuwarsa kan karuwar yawan yara kanana da basu zuwa makaranta a Najeriya.

Obaseki ya yi wannan furucin ne yayin da ya karbi bakuncin ministan Ilimi, Adamu Adamu, da shugabannin hukumar bada ilimi a matakin farko ta kasa da ta jiha a ofishinsa ranar Talata.

Kara karanta wannan

Babu unguwar da babu yan kwaya a Najeriya, Janar Buba Marwa

Gwamnan Edo, Godwin Obaseki
Gwamnan PDP ya bi sahun Sheikh Gumi, Ya Bayyana hanyar da Buhari zai bi ya kawo karshen yan bindiga Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

The Cable ta rahoto Gwamnan yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Idan bamu maida hankali wajen inganta ilimi ba, muka gyara tsarin ilimin mu tun daga matakin farko, to wannan matsalar ta yan bindiga da muke fama da ita zata zama almara a shekara 10-20."

Matakin da ya kamata Buhari ya dauka

Obaseki ya yi kira ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya soke hukumar UBEC matukar ta gaza maida kashi 50% na yara makaranta.

A cewarsa gwamnatinsa ba ta da wani zabi da ya wuce inganta ilimi a matakin farko saboda yaran dake kammala sakandire na komawa sana'ar aski ne ko siyar da dukiyoyinsu.

Matsalar fitar yan Najeriya kasashen waje

Gwamna Obaseki ya koka kan yadda yaran dake kammala sakandire ke maida hankali wajen tara kudi domin wani ya musu alƙawarin kai su wata kasa a waje.

Kara karanta wannan

Gombe: Gwamna Inuwa Yahaya ya haramta wa makiyaya shiga jihar

"A halin yanzun muna da matasa maza da mata kusan 30,000 yan asalin Edo sun koma Libya, suna jiran a ketara da su kasashen turawa."
"Idan suna da ilimi kuma zasu iya tunani, karatu da rubutu, za su tambayi kansu dalilin da yasa zasu fice zuwa wata ƙasa."

A wani labarin kuma Pantami yace Nan gaba kadan Najeriya zata shiga sahun kasashen duniya mafi karfin tattalin arzikin zamani

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Pantami, yace nan gaba kadan za'ai mamakin matakin da Najeriya zata hau.

A cewarsa tattalin arzikin zamani na Najeriya zai shiga sahun mafi karfi a duniya nan da wasu shekaru kalilan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel