Gombe: Gwamna Inuwa Yahaya ya haramta wa makiyaya shiga jihar

Gombe: Gwamna Inuwa Yahaya ya haramta wa makiyaya shiga jihar

  • Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya haramta wa makiyaya shiga jihar har sai bayan watan Janairu
  • Hakan wani yunkuri ne na kawo karshen rikicin manoma da makiyaya da ake yawan samu duk shekara wanda ke sanadiyar asarar rayuka da dukiyoyin jama'a
  • Hakazalika gwamnatin ta jihar Gombe ta haramta wa kananan yara yin kiwo

Gwamnatin Gombe karkashin Inuwa Yahaya ta kafa wata doka na hana makiyaya da ke wajen jihar shiga cikinta har sai bayan watan Janairun 2022.

An dauki wannan matakin ne da nufin kawo karshen tashe-tashen hankula da ake yawan samu tsakanin manoma da makiyaya a duk shekara wanda ke sanadiyar rasa rayuka da dukiya, rahoton Aminiya.

Gombe: Gwamna Inuwa Yahaya ya haramta wa makiyaya shiga jihar
Gombe: Gwamna Inuwa Yahaya ya haramta wa makiyaya shiga jihar Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Kwamishinan Tsaro na Jihar, Adamu Dishi Kupto, ya shaida wa BBC cewa gwamnatin jihar kuma ta hana kiwon dare, lokacin da ya ce aka fi yin barna da kuma hana wa yara kanana kiwo.

Kara karanta wannan

Har bayan wata 7, an kasa sasanta rikicin Kwankwaso da Wali a PDP

Sashin Hausa na BBC ya kuma rahoto cewa kwamishinan tsaro na jihar, Adamu Dishi Kupto, ya sanar masa da cewa gwamnatin ta kuma hana kiwon dare.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa a wannan lokacin ne aka fi yin barna sannan kuma an hana kananan yara yin kiwo.

Kupto ya ce:

"A yanzu manoma ba su nome amfanin gonarsu ba, idan aka bari makiyaya suka shigo za su yi barna, wannan dalilin ne ya sanya gwamnati ta kafa dokar."

Makiyaya sun miƙa wa ƴan sanda ɗan uwansu, Jabir Nuhu, bayan ya kashe manomi

A wani labari na daban, makiyaya sun mika wa yan sanda dan uwansu mai suna Jabir Nuhu kan zarginsa da kashe wani manomi a kauyen Bada da ke karamar hukumar Dukku a jihar Gombe.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a makon da ta gabata bayan rashin jituwa ya shiga tsakanin Nuhu mai shekaru 15 da wani manomi saboda zargin kutsa masa gona.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Yadda aka kusa halaka zababben gwamnan Anambra saura wata 8 zabe

A cewar majiyar, manomin ya fusata bayan Nuhu ya ki bin umurninsa na cewa kada ya kutsa masa ta cikin gona, hakan yasa ya kama Nuhu da dambe, shi kuma ya daba wa manomin wuka a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel