Da Dumi-Dumi: Wani gini ya sake kifewa a Jihar Legas, Mutane da dama sun mutu

Da Dumi-Dumi: Wani gini ya sake kifewa a Jihar Legas, Mutane da dama sun mutu

  • Bayan kifewar gini mai hawa 21 a jihar Legas, a yau Laraba an sake samun wani gini da ya rushe kan jama'a a yankin Badagry
  • Rahoto ya nuna cewa tuni jami'an kwana-kwana da masu ceto suka dira wurin, kuma an ceto wasu mutum 5 a raye
  • Daraktan hukumar kwana-kwana ta jihar Legas ta tabbatar da cewa an kuma ceto wasu hudu da ko motsi ba su yi

Lagos - Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wani gini da ake cikin aikin gina shi ya kife a Magbon, yankin Badagry, jihar Legas yau Laraba, inda ake tsammanin mutum hudu sun mutu.

Hakanan kuma an zaro wasu mutum biyar ɗauke da raunuka kala daban-daban, yayin da jami'ai ke cigaba da aikin ceto sauran.

Wannan na zuwa ne bayan dogon gini mai hawa 21 ya kife a jihar a farkon wannan watan, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.

Read also

Shugaba Buhari ya dawo Najeriya bayan ziyarar aiki Birtaniya, Faransa da Afrika ta kudu

Kifewar gini
Da Dumi-Dumi: Wani gini ya sake kifewa a Jihar Legas, Mutane da dama sun mutu Hoto: Tribuneonlineng.com
Source: UGC

Hukumar kwana-kwana ta tabbatar

Daraktan hukumar kashe gobara (Kwana-kwana) ta jihar Legas, Margret Adeseye, ta tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta bayyana cewa tuni jami'an kwana-kwana da masu aikin ceto na ofishin Badagry, suka dira wurin jim kaɗan bayan samun rahoton lamarin.

Daraktan tace:

"Mun samu rahoton rushewar wani gini a Badagry, jahar Legas. Tuni jami'an kwana-kwana suka ceto mutum 5, yayin da ake cigaba da aikin ceto sauran waɗan da ginin ya rufta wa."
"Mafi yawan mutanen da lamarin ya shafa masu aikin gini ne a wurin, kuma an zaro su da rauni daban-daban amma suna cikin hayyacinsu, an garzaya da su asibiti."
"A halin yanzun an ciro wasu mutum hudu ko motsi basu yi, kuma zuwa yanzun jami'an yan sanda da yan kwana-kwana na cigaba da aiki a wurin."

Read also

Fastocin kamfe na Sanata Kalu sun yadu a kudu, zai tsaya takarar shugaban kasa a APC

Gini a Legas
Da Dumi-Dumi: Wani gini ya sake kifewa a Jihar Legas, Mutane da dama sun mutu Hoto: vanguardngr.com
Source: UGC

A wani labarin kuma Batun Jaruma Rahama Sadau da wasu sabbin muhimman abubuwa 4 da suka faru a Kannywood

A wannan makon an samu wasu muhimman abubuwa guda 5 masu muhimmanci da suka faru a Kannywood.

Daga cininsu shine batun raɗin sunan jaririyar da aka haifa wa Adam A. Zango, da kuma abinda ya shafi Rahama Sadau.

Source: Legit.ng

Online view pixel