'Yan aware daga Kamaru sun shigo Najeriya, sun kashe mutane, sun kone gidaje

'Yan aware daga Kamaru sun shigo Najeriya, sun kashe mutane, sun kone gidaje

  • Wasu 'yan awaren kasar Kamaru sun shigo wani yankin Najeriya, inda suka hallaka wasu mutane a jihar Taraba
  • Sanata mai wakiltar yankin a Taraba ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce akwai bukatar kawo dauki a yankin
  • Kana ya bayyana irin yawan barnar da 'yan ta'addan suka yi tare da bayyana cewa har yanzu ba a san manufar shigowarsu ba

Taraba - Daily Trust ta ruwaito cewa, wasu da ake zargin 'yan awaren Ambazonia ne daga kasar Kamaru sun yi barna a karamar hukumar Takum da ke jihar Taraba.

A cewar mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Emmanuel Bwacha, wadanda ake zargin sun bindige hakimin kauye da wasu mazauna unguwar Manga.

Kauyen Manga yana da tazarar kilomita 20 daga Dam din Kashimbilla.

Kara karanta wannan

Yajin aikin ASUU: Kakakin majalisa ya gayyaci ministar kudi, na ilimi da shugaban ASUU

Da dumi-dumi: 'Yan aware daga Kamaru sun shigo Najeriya, sun kashe mutane
'Yan awaren Ambozinia na kasar Kamaru | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, sanatan, ya tabbatar da lamarin a zaman majalisar dattijai a ranar Laraba, ya ce an kashe mutanen ne a yayin farmakin da ‘yan awaren Kamaru suka kai yankin, inda suka kuma rusa kauyen.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bwacha, mai wakiltar Taraba ta Kudu a majalisar dattawa, ya ce mamayewar ‘yan awaren na iya zama barazana ga yankunan Najeriya saboda har yanzu ba a san dalilin shigowarsu ba.

Don haka ya yi kira ga sojoji da su gaggauta daukar mataki domin dakile mamaye al’ummar Manga da ‘yan awaren ke yi.

Ya ce:

“Na tashi da safen nan ne domin in jawo hankalin ‘yan kasarmu musamman jami’an tsaro kan wannan mummunan lamari da ke dumfaro ci gaban kasarmu.
“Karamar hukumar Takum tana dauke da bataliya ta 23 ta sojojin Najeriya, don haka mai girma shugaban kasa, cikin girmamawa ina cewa sojojin Najeriya ya kamata su tashi tsaye wajen dakile wannan bala’i a yankin.

Kara karanta wannan

Jami'ar Ilorin ta kori dalibin dan aji hudu da ya lakadawa lakcararsa dukan kawo wuka

“Har yanzu ba a san dalilin shigowarsu ba (’yan aware), ko suna son fadada yanki ne ko kuma da’awar mamaye kudu maso yammacin Kamaru.
“Yayin da nake magana, mutane da dama sun bata kuma har yanzu ba a san inda suke ba. An kuma ruguza kauyen.”

Bayan haka, Majalisar Dattawa ta yi shiru na minti daya don karrama wadanda 'yan awaren Ambazonia daga Kudancin Kamaru suka kashe a yankin Manga.

An samu fashewar bama-bamai biyu a Kampala, babban birnin kasar Uganda

A wani labarin, an ji fashewar wasu bama-bamai biyu a birnin Kampala, babban birnin kasar Uganda.

Wani Derby Awio, mazaunin Kampala ne ya tabbatar wa jaridar TheCable faruwar lamarin da safiyar yau Talata.

Awio yace: "Ba ma cikin kwanciyar hankali a Kampala."

Asali: Legit.ng

Online view pixel