Gwamnatin Tarayya ta bayyana abin da ya sa mutane suke wahala, ba su samun abin yi

Gwamnatin Tarayya ta bayyana abin da ya sa mutane suke wahala, ba su samun abin yi

  • Ma’aikatar ilmi ta hada kai da SKYE, sun shirya wani taro yau a Abuja domin a yaki zaman banza.
  • Gwamnatin Tarayya ta shirya wannan ne domin a rage matsalar zaman kashe wando a Najeriya.
  • Sonny Echono yace ana yaye wadanda suka kammala manyan makarantu da ba su san kan aiki ba.

Abuja - Gwamnatin tarayya tayi bayanin abin da ya sa miliyoyin matasan da suke shan wahala, suna fama babu rashin aikin yi bayan sun yi karatu.

Gwamnatin tarayya tace wadanda suka gama makaranta ba su saman aikin yi ne domin ba su da kwarewar da ake bukata wajen daukar mutane aiki.

Jaridar Vanguard tace Sakataren din-din-din na ma’aikatar ilmin tarayya, Sonny Echono ya bayyana wannan da yake jawabi a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Borno: Dan majalisa a ya bayyana yadda 'yan ISWAP suka kone gidan da ya ginawa dan uwansa

A ranar Alhamis, 11 ga watan Nuwamba, 2021, Arch. Sonny Echono ya gabatar da jawabi a wajen wani taron kwana biyu da hukumar TVET ta shirya.

Sonny Echono yake cewa rashin kwarewar wadanda suka kammala karatu ya jawo an samu karancin masu ilmi da suka san kan aiki a Najeriya.

Gwamnatin Tarayya
Matasa a Najeriya Hoto: www.mirror.co.uk
Asali: UGC

Shirin Skills Development for Youth Employment

Ma’aikatar ilmin tarayya da hadin-gwiwar tsarin SKYE da aka shigo da shi domin a horas da matasa suka shirya wannan taro na tsawon kwana biyu.

“Mafi yawan daliban da ake yayewa a jami’o’i da makarantun koyon aiki da kwalejin horo a kasar nan ba su bada ilmin da ake bukata wajen neman aiki.”
“Wannan ya yi sanadiyyar da ake samun miliyoyin dalibai da ake yaye da ba su da aikin yi.” - Sonny Echono.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar Gwamnati ta sasanta da Nnamdi Kanu da Igboho a wajen kotu – Malami

Echono ya cigaba:

“Babu shakka akwai gibi tsakanin kwararrun mutanen da ake da su da wadanda ake bukata. Najeriya tana fuskantar kalubale wajen samar da aikin yi”

Babban jami’in gwamnatin yake cewa wannan ya jawo aka bar Najeriya a baya wajen cigaba. Arch. Echono yace wannan matsala ce ga gwamnatin kasar.

A cewar Echono, gwamnatoci suna bakin kokarin wajen ganin an horas da matasa ta hanyar kirkiro makarantun koyor da aiki da cibiyoyin VEI da IEI da MSTC.

Aliko Dangote ya lula

A yau ake jin cewa alkaluman bloomberg billionaires index sun nuna yanzu Alhaji Aliko Dangote ne mutum na 102 a cikin sahun manyan masu kudin Duniya.

Daga fam Dala Biliyan 17.8, yanzu Mai kudin na Afrika ya mallaki Dala Biliyan 19.8. Ana hasashen cewa dukiyar mai kudin Afrikan a yau ta haura Naira tiriliyan 8.

Asali: Legit.ng

Online view pixel