'Yan sanda sun yi ram da wasu samari 2 bayan sun datse wa juna hannaye yayin kwasar dambe

'Yan sanda sun yi ram da wasu samari 2 bayan sun datse wa juna hannaye yayin kwasar dambe

  • ‘Yan sanda sun kama Adamu Mohammed da Bukar Audu bayan sun datse wa juna hannaye yayin kwasar dambe a Garin Alkali, karamar hukumar Dapchi da ke jihar Yobe
  • Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim ya bayyana hakan a wata takarda da ya saki a ranar Litinin a Damaturu inda ya ce da misalin 8:30pm su ka samu labarin faruwar lamarin
  • A cewarsa dukan su shekarun su 25 kuma dama ana zargin ‘yan wata kungiyar ‘yan ta’adda ne a yankin su kuma ba a san musabbabin fadan ba saboda su na asibiti rai a hannun Allah

Jihar Yobe - ‘Yan sanda sun yi ram da samari 2 bisa kama su dumu-dumu da laifin sare wa juna hannaye, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

An ruwaito yadda ‘yan sandan su ka kama Adamu Mohammed da Bukar Audu, bayan sun datse wa juna hannaye yayin wani fada da su ka tafka a Garin Alkali, karamar hukumar Dapchi da ke jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun kashe babban soja, AVM Muhammad Maisaka tare da jikansa a Kaduna

‘Yan sanda sun damke samari 2 bayan sun datse wa juna hannaye yayin kwasar dambe
‘Yan sanda sun damke samari 2 bayan sun datse wa juna hannaye yayin kwasar dambe. Hoto: Daily Trust

Premium Times ta bayyana yadda Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, a ranar Litinin a Damaturu ya bayyana a wata takarda.

Abdulkarim ya ce wadanda ake zargin duk shekarun su 25, an kuma gano cewa duk ‘yan wata kungiyar ‘yan ta’adda ne.

A cewar Abdulkarim:

“An kama wadanda ake zargin bayan labari ya iso wa ‘yan sanda da misalin karfe 8:30pm, cewa sun yi fada da adduna da sanduna kuma sun yi kare jini biri jini.
“Sakamakon fadan sun datse wa juna hannaye.
“Har yanzu ba a gano dalilin fadan ba don yanzu haka su na nan rai a hannun Allah a asibitin tarayya na FMC Nguru ana kulawa da su.”

Kakakin ‘yan sandan ya ce har yanzu a na ci gaba da bincike akan lamarin inda ya kara da cewa ‘yan sanda su na ci gaba da karfafa tsaro a wuraren don gudun barkewar rigima.

Kara karanta wannan

Lamari ya yi muni yayin da matasa suka ba hammata iska, suka datse hannayen juna

Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba

A wani rahoton, wata kotun majistare ta daure wani matashi, Lekan Alaka, mai shekaru 19, watanni 3 bisa satar kujerun roba masu kimar N91,200 daga cocin Mount Zion Angelican.

‘Yan sandan sun kama Alaka da laifin sata kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Alkali Olajumoke Somefun ya yanke hukunci bisa tabbatar da laifin da ya aikata bisa ruwayar Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel