'Yan ta'addan ISWAP sun kai hari sansanin soji a Borno, suna ta musayar wuta da sojoji

'Yan ta'addan ISWAP sun kai hari sansanin soji a Borno, suna ta musayar wuta da sojoji

  • Rahotonni sun bayyana cewa, a halin yanzu 'yan ta'addan ISWAP na can na barna a wani yankin jihar Borno, Arewa maso gabas
  • An ce an ga suna kan hanyar Kai hari Askita/Uba, amma ba a dauki mataki ba har suka aiwatar da barnar da suka zo yi
  • Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar tga Borno ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya bayyana yadda lamarin ya faru

Borno - Wasu 'yan ta'adda da ake zargin mayakan ISWAP ne a halin yanzu suna musayar wuta da sojoji a wani sansanin soja da ke karamar hukumar Askira/Uba a jihar Borno.

Wasu mazauna sun ce sun hango mayakan na ISWAP a cikin wani dogon ayarin motocin bindigu a hanyar Ngude zuwa Askira, da sanyin safiyar yau.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya har sun gaji da kuka, kashe-kashen rayuka ya zama ruwan dare: Yakubu Dogara

Yanzu-Yanzu: 'Yan ta'addan ISWAP na can na musayar wuta da sojoji a Borno
'Yan ta'addan ISWAP | Hoto: dailynigerian.com
Asali: Twitter

Jama'a da dama sun tsere cikin daji yayin da wasu suka makale a gidajensu.

Adamu Saleh ya shaida wa The Sun cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Al’amarin ya yi muni amma ‘yan ta’addan sun janye a yanzu.”

Mazauna sun yi ikirarin cewa sun kai rahoton zirga-zirgar 'yan ta'addan ga jami'an tsaro amma ba a dauki wani mataki ba kafin wannan mummunar kungiyar ta afkawa garin Askira bayan sa'o'i.

Yayin da yake tabbatar da hare-haren, Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Engr Abdullahi Musa Askira, ya shaida wa Daily Trust cewa a halin yanzu ‘yan ta’addan da sojoji suna musayar wuta.

A cewarsa:

“Eh, a halin yanzu ISWAP sun kai hari garin Askira. An sanar da ni cewa sojojinmu suna fafatawa da su, amma mazauna su tsere cikin daji.
"Mutane na sun gaya mani cewa maharan sun zo ne da motoci kusan 16 kuma ana cikin rudani a fadin garin a yanzu."

Kara karanta wannan

Zamfara: Ƴan bindiga sun yi wa dagaci yankan rago a gaban jama'a, kun kashe wasu 8

Wani jami’in sa kai na JTF, Yakubu Luka, ya ce nan take maharan suka far wa garin, inda suka tunkari sansanin sojoji.

"Muna sa ran samun tallafi daga al'ummar da ke kusa, yayin da nake magana da ku ana ci gaba da harbi da manyan bindigogi."

Yakubu yace:

“Muna kira ga hukumomi da su aika da jiragen yaki domin tallafawa sojojin kasa. An fi karfinmu; manyan motocin bindiga biyar ne kawai muke da su.”

Boko Haram sun farmaki wani gari a Borno, sun kone gidaje da dukiyoyi

A wani labarin, mazauna garin Askira da ke karamar hukumar Askira Uba a jihar Borno sun tsere lokacin da mayakan Boko Haram suka kai hari wani kauye ranar Laraba.

Daily Trust ta ce ta samu labari daga majiyoyi cewa ‘yan ta'addan da suka kai harin da safe sun kona gidaje da dama.

Wani ganau ya ce maharan sun kai farmaki a yankin Krangla, mai tazarar kilomita takwas da garin.

Kara karanta wannan

Gagarumar Nasara: Sojojin Najeriya sun hallaka yan ta'adda 31, sun damke 71, wasu 1,186 sun mika wuya

Asali: Legit.ng

Online view pixel