N2tr CBN ta rarraba wa masu kananan sana'o'i da kamfanoni a cikin shekara 1, Emefiele

N2tr CBN ta rarraba wa masu kananan sana'o'i da kamfanoni a cikin shekara 1, Emefiele

  • Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin Najeriya ya ce sun rabawa 'yan Najeriya bashin tiriliyan biyu zuwa uku domin rage radadin korona
  • Kamar yadda ya bayyana, an rarrabawa masu sana'o'in cikin gida, kanana, matsakaita da manyan sana'o'i tallafi a cikin shekara 1
  • Emefiele ya ce wadanda aka bai wa bashin za su fara biyan kudin domin bashi ne, ba kamar yadda wasu ke tsammanin sun ci bulus ba

Gwamnan Babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele a ranar Talata ya ce an rarraba tsakanin tiriliyan biyu zuwa uku ga masu kanana, matsakaita da manyan masana'antu daga shekarar da ta gabata zuwa yanzu domin basu damar farfadowa da ga illar annobar korona.

Emefiele ya bayyana hakan a wata tattaunawa da aka yi da shi a kasuwar duniya ta kasashen Afrika da aka yi a Durban, Afrika ta kudu, Sunnews ta wallafa.

Kara karanta wannan

Rikicin VAT: Gwamnatin Buhari na tunanin sasantawa da Wike da Gwamnonin Kudu ta huta

N2tr CBN ta rarraba wa masu kananan sana'o'i da kamfanoni a cikin shekara 1, Emefiele
N2tr CBN ta rarraba wa masu kananan sana'o'i da kamfanoni a cikin shekara 1, Emefiele. Hoto daga sunnewsonline.com
Asali: UGC

Kamar yadda yace, Najeriya ta fuskanci illar annobar a shekarar da ta gabata, hakan yasa shugaban kasa Buhari ya kira shi da ministar kudi inda ya umarcesu da a fitar da tsarin tallafin rage radadin annobar korona.

Sunnews ta wallafa cewa, Gwamnan babban bankin ya ce tallafin bashi wanda daga baya aka kara yawan wadanda aka bai wa, bashi ne ba wai kyauta ba kamar yadda wasu suke kallo.

"Mun raba N3 tiriliyan daga shekarar da ta gaba ta zuwa wannan shekarar. Mun bai wa manoma, masu sana'ar cikin gida da sauran wadanda ba su samun bashi. Za su fara biya bayan shekaru 2. Muna da duk wata shaida da za ta nuna cewa mun yi abinda ya dace," yace.

Gwamnan babban bankin Najeriya ya ce tabbas ba za a rasa kuskure ba wurin kula da tattalin arziki, ballantana a lokacin annobar korona amma ba manyan kura-kurai ba.

Kara karanta wannan

Rahoton EndSARS: HURIWA ta bukaci Buhari ya fatattaki Lai Mohammed kan karyar da ya zuga

Ya ce an koyi darussa masu yawa kuma wadannan kura-kuran ba za su sake maimaita kansu ba.

Ya tabbatar da cewa, a sauran shekarun da suka rage wa mulkin da kuma wa'adinsa, za su mayar da hankali wurin samar da ababen more rayuwa da kuma samar da ayyuka wanda zai habaka tattalin arziki tare da shawo kan matsalar tsaro.

Buhari ya sha alwashin daukan mataki kan 'yan bindiga, barazana ga rashin abinci

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace mulkinsa zai yi amfani da duk wata dama da dabaru da ya sani wurin yin maganin 'yan bindiga domin tabbatar da samuwa abinci a damina mai zuwa.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, shugaban kasan ya sanar da hakan ne ga manema labarai na gidan gwamnati jim kadan bayan kammala sallar idi a ranar Alhamis.

Kamar yadda yace, matsalar 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane za a shawo kanta domin tabbatar da cewa kasar bata fada kalubalen rashin abinci ba.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro, ambaliya da dalilai 4 da suka jawo tsada da hauhawan farashin abinci

Asali: Legit.ng

Online view pixel