Rikicin VAT: Gwamnatin Buhari na tunanin sasantawa da Wike da Gwamnonin Kudu ta huta

Rikicin VAT: Gwamnatin Buhari na tunanin sasantawa da Wike da Gwamnonin Kudu ta huta

  • Gwamnatin tarayya za ta duba yiwuwar sasantawa da gwamnonin jihohi a game da harajin VAT
  • Wasu Gwamnonin kudu suna ikirarin ba aikin hukumar FIRS ba ne karbar VAT, sun kai maganar kotu
  • Zainab Ahmed ta nuna da wuya a karasa shari’ar, za ta san yadda za ayi, ayi sulhu a wajen kotun

Abuja - Gwamnatin tarayya tana tunanin yadda za ta sulhunta da jihohin da suka kai ta kotu domin raba gardamar wanda yake da hakkin karbar VAT.

Ministar tattali, kasafi da tsare-tsaren arzikin kasa, Zainab Ahmed, ta bayyana wannan ne a ranar 12 ga watan Nuwamba, 2021, da aka yi wata hira da ita.

Zainab Ahmed ta tattauna da ‘yan jarida a wani shirin siyasa da ake yi a gidan talabijin na Channels.

Kara karanta wannan

Rahoton EndSARS: HURIWA ta bukaci Buhari ya fatattaki Lai Mohammed kan karyar da ya zuga

Ministar tace karar da aka shigar a kotu ba zai iya shawo kan sabanin ba, don haka ya zama dole gwamnatin tarayya tayi sulhu ta siyasa da gwamnonin.

Kotu ba za ta iya kawo mafita ba - Ahmed

Ahmed ta nuna cewa Alkali ba zai iya raba gardama a kan wanda ya kamata a bari da nauyin karbar harajin VAT ba, don haka za a tattauna a kan teburi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnoni a Arewa
Gwamnoni tare da Buhari Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Jaridar Premium Times tace ganin maganar tana kotun koli a halin yanzu, Ministar tattali da kasafin arzikin tace bai kamata ta rika yin magana a kai ba.

Me Ministar ta fadawa 'yan jarida a hirarsu?

“Dole in yi taka-tsan-tsan da wannan domin batun su na kotu, kuma bai kamata in rika magana a kan abin da ya kai gaban kotu ba.” – Ahmed.

Kara karanta wannan

Borno: Dan majalisa a ya bayyana yadda 'yan ISWAP suka kone gidan da ya ginawa dan uwansa

“Amma ina sa ran cewa matsala ce da za a kawo karshenta, ta hanyar zama a tebur, ba da surutu a shafukan jaridu ba, ba kuma ta hanyar shari’a ba.”
“Kwarai, za a nemi mafita ta siyasa. Muna kokarin ganin yadda za mu yi sulhu a wajen kotu.”

Ko da wasu gwamnonin kudu su na kalubalantar gwamnatin tarayya a kan karbar haraji, Ahmed tana sa ran samun Naira tiriliyan 2.2 daga VAT a shekarar 2022.

PDP ta bar sakatariya saboda kudin haya

A ranar Litinin ne aka ji kotu ta bada umarni a fatattaki jam’iyyar PDP daga ofishinta na jihar Legas saboda an kai ta kara cewa ta gagara biyan hayar shago.

Bashi ya taru a kan wuyan shugabannin PDP, wannan ya sa mai gidan da ake haya ya shigar da karar jam'iyyar hamayyar a kotu, kuma ya yi nasara aka kore su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel