Rashin tsaro, ambaliya da dalilai 4 da suka jawo tsada da hauhawan farashin abinci

Rashin tsaro, ambaliya da dalilai 4 da suka jawo tsada da hauhawan farashin abinci

  • Kaduna - Abubakar Sani Abdullahi ya yi rubutu na musamman, inda ya yi bayani a game da abubuwan da suka haddasa tashin kayan abinci a halin yanzu.
  • Abubakar Sani Abdullahi malami ne a sashen kula da noma da tattalin arzikin kasa a cibiyar binciken harkokin noma ta Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.
  • Legit.ng Hausa ta kawo wannan rubutu da masanin tattalin harkar noma ya yi a shafinsa:

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai. Muna godewa Allah da yabamu damina mai albarka.

Magidanta da sauran bayin Allah za su ga canjin da yake wakana kullum ta fannin tsada na kayan abinci musamman a yanzu lokacin kaka da ana girbi, ko an gama girban wasu amfanin gona. Amma duk da haka abubuwan kayan abinci sai kara tsada sukeyi.

Kara karanta wannan

Gumi ya caccaki 'yan aware: Igboho da Kanu ne suka kunna wutar rikicin Fulani a kudu

Na samu lokaci na zagaya wasu Jihohin da aka fi noma kayan abinci a fadin Arewa musamman masara, shinkafa, gero, dawa da wake. Daga cikin abubuwan da na iya zakulowa bayan hirarraki da nayi da manoma da kamfanoni masu sarrafa kayan abinci, na fito da wasu manyan sakamako kamar haka:

Me suka haddasa tsadar farashi a yau?

1. Rashin Tsaro ko karancin tsaro

Idan ka dauki Jihar Kaduna a misali, duk Fadin Najeriya babu inda ya kai wannan Jiha noma masara, amma saboda yawan garkuwa da mutane, mutane da yawa basu shiga ko sharan gona ba ballantana suyi noma ba, musamman manoma da wasu daga cikin ma'aikatan gwamnati da suke noma abinda zasuci su da iyalansu.

Tsoro ya sa mutane sun guji gonakin su. Idan kazo ka dauki Neja, Katsina,Sokoto da Zamfara, da yawa daga cikin manoma basu shiga gonaki ba. Saboda tsoron garkuwa da mutane, wasunsu sun koka cewa shekaran da ta wuce, sai da suka biya haraji ga masu garkuwa, sannan aka bari suka shiga suka girbi amfanin gonakin su.

Kara karanta wannan

Borno: Dan majalisa a ya bayyana yadda 'yan ISWAP suka kone gidan da ya ginawa dan uwansa

2. Ambaliyan ruwan sama

A cikin watan bakwai da watan takwas, akwai wasu yankuna da na zaga naga yadda ruwa yake tafiya da gonaki 300-500 a kauye guda, musamman masu gonakin shinkafa, masara, gero da dawa. Wannan ambaliya da aka samu ya sa gonaki da yawa a yankunan Bauchi, Gombe, Jigawa, Kebbi duk anyi asarar amfanin gona. Kuma babu daman dawo da shuka domin ana tsakiyar damina.

Gonaki
Wata gona a Najeriya Hoto: www.businesslist.com.ng
Asali: UGC

3. Fari

Ruwan bana ya tsaya lokacin da ba a yi tsammani ba yayin da wasu amfanin gonakin suna kan gaban su na karasawa da nuna, amma ruwa ya dauke musu. Da yawa daga cikin gonakin shinkafa sun kone kamar wuta aka cinna musu. Haka dawa, gero da masara a wasu Jihohin.

4. Kamfanonin abincin dabbobi

Akwia gasa tsakanin gidaje da kuma kamfanonin sarrafa kayan abincin dabbobi. 60% na masaran da ake nomawa yana tafiya e ga kamfanonin sarrafa kayan abincin kaji da kifi ne. Sannan 20% shi muke surrafawa domin yin tuwo da sauransu a gidajenmu. Sai 20% ya kan tafi ga kamfanoni masu sarrafa fulawa da garin masara.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Jami'an tsaro da 'yan IPOB sun shafe sa'o'i uku suna musayar wuta

Wannan gasa za a same shi a bana sosai, idan muka yi nazari zamu ga kusan babu jihohi da ba a karbar masara ko dawa ko waken suya. Muna da manyan kamfanoni irin su Flour Mills of Nigeria, Olam, Grand Cereals da sauran su. A yanzu haka sun fara karbar masara, wasunsu kuma suna jiran su fara sarrafa kayan abincin kaji da sauran su. Kusan ko wannensu yana bukatar kaya sosai domin hangen yadda tsadan kayan yake wanda dalilan karancin kayan ya jawo.

Menene abin yi ga magidanta?

I. Dole sai mun dawo munyi noman rani musamman a Yankunan da Allah ya ba su ruwan yin wannan noman.

II. Duk manomin da yayi noma bana, ya guji gaggawar rabuwa da abin da ya noma.

III. Sace-sacen amfanin gona zai karu a bana, duk wanda yayi girbi dole ya dauko amfaninsa da wuri daga gona.

IV. Yanzu ne ya dace ka sayi duk kayan abincin da kake amfani da shi, kada ka jira tsammani zai yi sauki nan gaba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da waɗanda suka tafi kai musu kayan abinci da kuɗin fansa a daji

Muna addua Allah ya kawo mana sassauci a cikin wannan rayuwar.

Kaya za su yi araha a shekara mai zuwa?

A baya kun ji labari cewa binciken masana ya bayyana dalilin da yasa 'yan Najeriya za su ci gaba da shan wahalar tsada wajen sayan hatsi da sauran kayan abinci.

Amma babban bankin ya yi hasashen cewa nan da shekarar 2022, farashin kayan abinci zai sauka da 10% cikin 100%, saboda mawuyacin halin da tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel