Buhari ya sha alwashin daukan mataki kan 'yan bindiga, barazana ga rashin abinci

Buhari ya sha alwashin daukan mataki kan 'yan bindiga, barazana ga rashin abinci

- Shugaba Muhammadu Buhari ya ce zai yi amfani da dukkan abinda yake da shi wurin shawo kan matsalar tsaro a kasar nan

- Yayi addu'ar samun damina tagari tare da komawar jama'a gona domin samun amfani na ci har da na siyarwa

- Shugaban kasan ya sanar da hakan ne bayan idar da sallar idi yayin da ya zanta da menama labaran gidan gwamnati

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace mulkinsa zai yi amfani da duk wata dama da dabaru da ya sani wurin yin maganin 'yan bindiga domin tabbatar da samuwa abinci a damina mai zuwa.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, shugaban kasan ya sanar da hakan ne ga manema labarai na gidan gwamnati jim kadan bayan kammala sallar idi a ranar Alhamis.

Kamar yadda yace, matsalar 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane za a shawo kanta domin tabbatar da cewa kasar bata fada kalubalen rashin abinci ba.

KU KARANTA: Haramta kiwo: Ndume yayi martani mai zafi ga Gwamnoni 17 na kudanci

Buhari ya sha alwashin daukan mataki kan 'yan bindiga, barazana ga rashin abinci
Buhari ya sha alwashin daukan mataki kan 'yan bindiga, barazana ga rashin abinci. Hoto daga @daily_trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Farmaki a Aso Rock: An gano dalilin da yasa aka kai hari fadar shugaban kasa

Shugaban kasan wanda yayi fatan samun damina mai kyau, ya ce: "Hukumomin tsaro suna aiki wurin dawo da karfin guiwar jama'a, ta yadda zasu koma gonakinsu.

"Wannan na da matukar amfani. Wannan ne abinda hukumomin ke yi a yanzu. Muna so jama'a su koma gona ta yadda zamu samu abinci isasshe a kasar nan har mu samu na fitarwa waje."

A yayin bayanin kokarin ganin shawo kan matsalar tsaro a kasar nan da mulkinsa ke yi, Buhari ya janyo hankali kan tarukan da ya dinga yi a makonnin da suka wuce inda yace hakan yana daga cikin matsayarsu da shugabannin tsaro.

A wani labari na daban, shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Abdulerasheed Bawa, yace dawo da tsohuwar ministan fetur, Diezani Alison Maduke gida tare da gurfanar da ita ba wasa bane.

Ya ce saboda tsohuwar ministar bata karkashin ikon Najeriya a yanzu tare da kalubalen da za a iya fuskanta wurin dawo da ita har yau sune manyan kalubale.

Wannan na kunshe a wata mujallar EFCC mai suna EFCC Alert wacce aka fitar a watan Afirilu, The Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng